An samu rabuwar kai a APC bayan gwamna Gaidam ya zabi magaji

An samu rabuwar kai a APC bayan gwamna Gaidam ya zabi magaji

- An samu rabuwar kawuna a jam'iyyar APC ta Yobe bayan gwamna mai barin gado ya zabi magajinsa daga yankinsa na Zone A

- Gwamna Ibrahim Gaidam ya zabi Alhaji Mai Mala Buni a matsayin wanda zai gaje shi sai dai hakan bai yiwuwa 'yan Zone B dadi ba domin sunce lokaci yayi da suma zasu dana mulkin

- Rashin gamsuwa da wannan zabin yasa Ibrahim Bamoi, daga Zone B ya kaddamar ta yakin neman zabensa kuma ya lashi takobin ganin shine zai zama dan takarar jam'iyyar a 2019

Sabuwar rikici ta bulla a jam'iyyar APC reshen jihar Yobe bayan gwamna mai barin gado, Ibrahim Gaidam ya zabi sakataren jam'iyyar na kasa, Alhaji Mai Mala Buni a matsayin wanda jam'iyyar za ta tsayar takara domin maye gurbinsa.

An samu rabuwar kai a APC bayan gwamna Gaidam ya zabi magaji
An samu rabuwar kai a APC bayan gwamna Gaidam ya zabi magaji
Asali: Depositphotos

Ko da ya ke jiga-jigan jam'iyyar da masu ruwa da tsaki sun amince gwamna Ibrahim Gaidam ya zabi dan takarar da jam'iyyar za ta tsayar a 2019, wani mai neman takarar, Ibrahim Bomoi, ya kaddamar da ofishin yakin neman zabensa a Damaturu tare da dimbin magoya bayansa a ranar Lahadi.

DUBA WANNAN: Hankula sun kwanta a Gundumbali bayan harin da Boko Haram suka kai - CJTF

Tsohon ma'ajin hukumar ayyukan cigaba na tarayya (FCDA) ya samu tarba daga dubban mutane magoya bayansa har sai da taron ya haifar da cinkoson motocci a baban titin Damaturu/Kano/Maiduguri.

Da yake amsa tambayoyin 'yan jarida, Direktan yakin neman zaben Bomoi a Zone B, Alhaji Salleh Jauro, ya ce yankin Zone A sun dade suna mulki a jihar na tsawon sama da shekaru 20. Ya soki yadda gwamna mai barin gado ya zabo magajinsa daga Zone A a maimakon ya bari 'yan takarar su fafata.

Sai dai duk da haka, Alhaji Jauro ya ce ba su da niyyar ficewa daga jam'iyyar, "maganar ficewa daga jam'iyya bai taso ba. Zamu tsaya cikin jam'iyar kuma mu tabbatar da cewa munyi nasara. Allah ne ke bayar da mulki kuma da izininsa dan takararmu Ibrahim Bamoi zaiyi nasara."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel