Yanzu-yanzu: Dan sarkin Musulmi ya samu mumunan hadarin mota bayan ya debi Codeine
Labarin da shigo mana yanzu daga majiyar Sahara Reporters na nuna cewa daya daga cikin yaran Sarkin Musulmi, Sultan Abubakar Sa'ad na biyu ya samu mumunan hadarin mota bayan sun debi kayan shaye-shaye na Kodin.
Yaron mai suna Amir ya debi mota da gudu misalin karfe 12 na rana wajen filin jirgin saman jihar Sokoto. Ya kasance a buge tare da wani abokinsa mai suna Khalifa Maccido da wata yarinya da suka kawo daga jihar Kaduna.
Idanuwan shaida sun bayyana cewa Amir na buge lokacin da yake tuki kuma an samu kwalban Benelyn Codeine.

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng