Jirgin kasa ya kashe shanu 52 a hanyar Abuja zuwa Kaduna
A yammacin yau, Lahadi, ne kwamishinan ‘yan sanda a jihar Kaduna, Ahmad Abdurahaman, ya tabbatar da cewar jirgin kasa dake jigilar fasinja daga Abuja zuwa Kaduna ya take wasu shanu 52 har lahira.
Da yake ganawa da manema labarai, Abdurahaman, ya ce hatsarin ya faru ne a garin Kasarami dake karamar hukumar Kagarko.
Ya kara da cewar shine ya jagoranci tawagar jami’an ‘yan sanda zuwa wurin hatsarin bayan an sanar da su.
“Sai dai da muka isa wurin sai muka iske cewar sabanin labarin da aka bamu na cewar an kai hari, sai muka iske cewar hatsarin jirgin kasa ne ya hallaka shanun.

Asali: Depositphotos
“Wasu Fulani ne ke son tsallakar da shanunsu kuma aka fada masu cewar jirgi ba ya aiki ranar Lahadi. A daidai lokacin da suke tsaka da tsallakar da shanun ne sai jirgi ya biyo hanyar tare da murkushe shanu 52.”
DUBA WANNAN: 2019: 'Yan takarar PDP 6 da zargin cin hanci ya yiwa dabaibayi
“Ina mai sanar da jama’a cewar maganar kai hari ba gaskiya bane kuma babu asarar ran mutum sai na shanu,” a kalaman kwamishinan na ‘yan sanda.
Kwamishina ya kara da cewa Fulanin na hanyar su ne ta komawa jihar Katsina lokacin da hatsarin ya afku tare da bayyana cewar ya yi taro da manoma da makiyaya na yankin domin tattaunawa da su a kan kiyaye afkuwar hakan a gaba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng