Za a dauki Ma'aikata 2000 domin Karantarwa a sabbin Makarantu 40 na jihar Borno

Za a dauki Ma'aikata 2000 domin Karantarwa a sabbin Makarantu 40 na jihar Borno

Mun samu cewa gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya bayar da umarni na gaggawa kan daukar sabbin ma'aikata 2000 aiki domin karantar da dalibai a matsayi malaman wasu sabbin Makarantu 40 da gwamnatin jihar ta kammala ginawa.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, gwamnatin ta daura wannan damara ne domin cike guraben dake reshen ma'aikatar ilimi na jihar.

Alhaji Yerima Saleh, shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar, shine ya bayyana hakan cikin birnin Maiduguri a ranar Asabar din da ta gabata yayin wata sanarwa da sanadin hadimin gwamnan akan hulda da manema labarai, Malam Isa Gusau.

Yake cewa, tuni gwamnatin jihar ta tanadi takardar neman aiki da sanadin ma'aikatar gwamnatin jihar ga dukkan mabukata aikin na karantarwa.

Za a dauki Ma'aikata 2000 domin Karantarwa a sabbin Makarantu 40 na jihar Borno
Za a dauki Ma'aikata 2000 domin Karantarwa a sabbin Makarantu 40 na jihar Borno
Asali: Facebook

Shugaban ma'aikatan ya bayyana cewa, ana bukatar kimanin ma'aikata 800 da suka kammala karatun digiri na farko musamman a fannin nazarin kimiya da kuma turanci yayin da ake bukatar wadanda suka kammala karatun su a kwalejan ilimi guda 200 wajen daukar aikin.

KARANTA KUMA: 'Yan Takara 12 dake neman Kujerar shugaban kasa, 120 sun mallaki fam din Kujerun Gwamna a jam'iyyar PDP

Gwamnatin kamar yadda rahotanni suka bayyana za ta dauki ragowar ma'aikatan 1000 bisa tsarin albashi mai kunshe da yarjejeniya ta yanayin aikinsu na tsawon wani wa'adi kayadadde.

Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar babban bankin duniya da kuma kungiyar kasashen Turai na ci gaba da bunkasa ci gaban jihar sakamakon tabarbarewar ta a sanadiyar rikita-rikitar ta'addanci na Boko Haram

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng