Gwamna Ayo Fayose amini na ne Inji Sanata Kwankwaso
A makon da ya gabata ne tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci Kudancin Najeriya inda yake cigaba da kamfen na neman kujerar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP.
Labari ya zo mana cewa ‘Dan takarar Shugaban kasar na PDP ya kai ziyara zuwa Kudu maso Yammacin Najeriya. Kwankwaso ya leka Jihohin Ondo, Ekiti da kuma Jihar Oyo inda yake neman ‘Yan PDP su ba shi goyon baya a zaben fitar da gwani.
Jirgin yakin neman zaben Rabiu Kwankwaso ya shiga babban Birnin Jihar Ekiti watau Ado-Ekiti inda ya zanta da Gwamna Ayodele Peter Fayose. ‘Dan takarar ya zauna da Gwamnan da ke shirin barin gado wanda ya kira babban Abokin sa.
KU KARANTA: Shekarau yace dole ta su su ka bar wa Kwankwaso PDP
Sanata Kwankwaso wanda yake neman goyon bayan 'Ya ‘yan PDP a zaben fitar da gwani da za ayi ya kuma zanta da manyan Jami’an Gwamnatin Ekiti a fadar Gwamnan. Ayo Fayose da kan sa ne ya tarbi Tawagar babban ‘Dan siyasar.
Kwankwaso ya kuma hadu da ‘Yan Majalisun dokoki da kuma na Tarayya na Jihar Ekiti tare da manyan ‘Yan Jam’iyyar PDP a gidan Gwamnatin. An yi wannan taro ne a Ranar Juma’a kamar yadda Hadiman Sanatan su ka bayyana mana.
Jirgin yakin neman zaben Sanata Rabiu Kwankwaso Kwankwaso ya leka Jihohin Ondo, Ekiti da kuma Jihar Oyo inda yake neman takarar PDP a 2019. Ranar Juma’a Kwankwaso da Fayose sun zauna game da zaben 2019 da za ayi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng