Dalilin da yasa arewacin Najeriya ya fi kudanci talauci - Masanin tattalin arziki

Dalilin da yasa arewacin Najeriya ya fi kudanci talauci - Masanin tattalin arziki

- Wani masanin tattalin arziki ya yi fashin baki dan dalilan da suka sa talauci ya fi tsananta a arewacin Najeriya idan aka kwatanta da kudu

- Masanin ya ce babban dalilin shine rashin hanyoyin samun kudaden shiga da jihohin arewa basu dashi

- Ya kuma lissafo karancin ilimi, yawan haihuwa, karkatar da kudin jama'a da 'yan siyasa keyi a maimakon samar da ababen inganta rayuwa

A wata hira da ya yi da BBC, wani masanin tattalin arziki ya ce jihohin da ke arewacin Najeriya sunfi takwarorinsu na kudu fama da matsanancin talauci ne saboda rashin samun kudaden shiga da ya kai na jihohin Kudun.

A cewar Dr Zahumnam Dapel, kudaden shiga da jihohin Legas da Ribas ke samu a shekara ya dara wandanda jihohi 14 na arewacin Najeriya ke samu, hakan kuma na nuna cewa gwamnatocinsu za su iya fitar da kudade domin inganta rayuwar al'ummarsu.

Dalilin da yasa arewacin Najeriya ya fi kudanci talauci - Masanin tattalin arziki
Dalilin da yasa arewacin Najeriya ya fi kudanci talauci - Masanin tattalin arziki
Asali: Facebook

Dr Dapel, wanda ya yi aiki a Amurka, ya cigaba da cewa yawan haihuwa ba tare da wadatuwa da arzikin da za su kula da yara da talakawan yankin arewa ke yi yana daya daga cikin ababen da ke kara radadin talauci a yankin.

DUBA WANNAN: Daya daga cikin masu son takarar shugaban kasa a PDP ya janye

Ya kuma ce kudancin Najeriya ta yiwa arewa fintinkau a fannin ilimi, inda ya ce a shekarar 1989 akwai jami'oi 12 a arewa yayin da kudu ke da 17, amma a kididigar da akayi a 2017 ya nuna cewa arewa na da jami'oi 58 yayin da kudu na da 102.

Masanin ya ce babu yadda za ka raba mutum da talauci muddin ba ka bashi ilimi ba.

Kazalika, ya ce karkatar da kudaden talakawa da 'yan siyasa da wasu ma'aikatan gwamnati keyi shima yana kara tsananta talauci a yankin.

Daga karshe, Dr Zahumnam ya shawarci gwamnati ta cigaba da taimakawa 'yan makaranta tare da samar da takin noma da inganta wutan lantarki da sufuri a kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags:
Online view pixel