Sojoji 3 sun rasa rayyukansu sakamakon sabuwar rikici da ta barke a Barikin Ladi

Sojoji 3 sun rasa rayyukansu sakamakon sabuwar rikici da ta barke a Barikin Ladi

- Wasu dakarun soji guda uku sun rasa rayyukansu a karamar hukumar Barikin Ladi da ke Jos

- Wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su waye ba ne suka kashe sojojin

- Kwamandan Operation Safe Haven da ke Filato ya ce wannan abin ba zai sake faruwa ba saboda ya dauki tsatsauran mataki

A kalla sojoji uku na 'Operation Safe Haven' suka ne suka rasa rayyukansa sakamakon wata hari da wasu 'yan bindiga suka kai a karamar hukumar Barikin Ladi da ke Jihar kamar yadda hukumar soji ta sanar a yau Asabar.

Augustine Agundu, wani manjo janar kuma kwamandan wata runduna a yakin ne ya tabbatar da rasuwar sojojin yayin da yake jawabi ga manema labarai a hedkwatan sojojin da ke Jos.

Rikicin Filato: An kashe sojoji uku a wata sabuwar hari da aka kai
Rikicin Filato: An kashe sojoji uku a wata sabuwar hari da aka kai
Asali: Facebook

Ya ce an kashe sojojin ne yayin da suke bakin aiki a karamar hukumar Barikin Ladi.

DUBA WANNAN: Daya daga cikin masu son takarar shugaban kasa a PDP ya janye

Kwamandan ya ce rikicin na jihar Filato yana daukan sabon salo fiye da yadda sojojin ke tsamani, abubuwan sun tabarbare tun kashe-kashen da suka faru a watan Yunin wannan shekarar.

Kwamandan ya cigaba da cewa mafi yawancin lokuta wasu marasa son zaman lafiya ne suke kitsa kashe-kashen wanda daga baya ake samun rasuwan rayyukan mutanen da basu-ji-basu gani ba.

"Ina Allah wadai da duk masu tayar da fitina a jihar Filato. Muna tattaunawa da shugabanin jama'a tare da shugabanin addinai da 'yan siyasa domin ganin an kawo karshe rikicin.

"Na rasa mutane uku. An kashe su ne sakamakon wata sabuwar rikici da ta barke. Abin takaicin shine yadda ake kara samun yaduwar makamai a hannun mutane. Babu inda ake magance fitina da fitina," inji shi.

Shugaban sojin ya ce abinda ya faru a Barikin Ladi ba zai sake faruwa ba saboda ya dauki tsatsauran mataki na sanya idanu a Barikin Ladi, inda ya kara da cewa babu wanda zai sake tayar da fitina.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel