Dan takarar shugaban kasa a PDP ya ja kunnen jam'iyyar

Dan takarar shugaban kasa a PDP ya ja kunnen jam'iyyar

- Jigo a PDP kuma tsohon shuagaban majalisar dattawa, David Mark, ya gargadi shugabanin jam'iyyar kan kakabawa jama'a dan takarar da basu so

- Mark ya ce muddin ba'a bawa 'yan jam'iyyar wanda suke so ba, za'a fuskanci riginginmu da rabuwar kawuna

- Dan takarar shugaban kasan kuma ya ce ya yi imanin zai iya kawo canji mai amfani a Najeriya shiyasa ya fito takarar

Dan takarar shugaban kasa a PDP ya ja kunnen jam'iyyar
Dan takarar shugaban kasa a PDP ya ja kunnen jam'iyyar
Asali: Depositphotos

Tsohon shugaban majalisar dattawa, kuma daya daga masu neman tikitin takarar shugabancin kasa a PDP, Sanata David Mark, ya yi kira ga jam'iyyar su guji aikita abubuwa da zasu janya rabuwan kai a jam'iyyar musamman yanzu da za'a gudanar da zaben deleget a cikin watan Satumba.

Ya kuma ja kunnen shugabani da masu ruwa da tsaki a jam'iyyar kan kakaba ma 'yan jam'iyyar dan takarar da basu so a tarukkan jam'iyyar ds za'ayi cikin watan Satumba zuwa Oktoba.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa na fice daga PDP - Tsohon Gwamna

A sanarwan da David Mark ya fitar a rannan Juma'a a Abuja, Sanatan ya shawarci 'yan jami'iyyar suyi biyaya da dokokin jam'iyyar wajen gudanar da zaben saboda gujewa barkewar fitina. Ya kara da cewa dole a bawa mutane wanda suke so.

Kalamansa: "Dole ne muyi biyaya ga dokokin jam'iyya wajen zaben fitar da deleget da za'a fara a ranar Asabar, ya kamata mu nunawa sauran 'yan kasa cewa jam'iyyar mu tana daraja demkradiyya wajen yin adalci da gaskiya."

Dan takarar shugaban kasan kuma ya sake jadada dalilin da yasa ya shiga takarar shugabancin kasar tun farko inda ya ce ya yi imanin cewa zai iya kawo canji na gari a Najeriya idan aka zabe shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel