Sojojin Najeriya sun kwato wasu mutane 21 daga hannun 'yan Boko Haram
- Sojojin Najeriya sun gano wata maboyar 'yan ta'addan Boko Haram
- Sojojin Najeriya sun kwato wasu mutane 21 daga hannun 'yan Boko Haram
- Sojojin Najeriya sun 'yan ta'addan su 14
Jami'an sojin Najeriya na rundunar Lafiya Dole dake fafatawa da 'yan ta'addan Boko Haram a yankunan jahohin Arewa maso gabashin Najeriya sun bayyana samun nasarar kubutar da akalla mutane 21 daga hannun 'yan ta'addan.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Shugaba Buhari shirin korar wasu kusoshin gwamnatin sa
Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da rundunar ta bakin jami'in hulda da jama'a da yada labarai na rundunarya fitar a garin Abuja.
Legit.ng ta samu haka zakika cikin sanarwar cewa dakarun sojin na Najeriya tare da taimakon mayakan sa-kai sun kuma kashe akalla 'yan Boko Haram din su 14 a wani samame da suka kai masu a maboyar su ta garin Gwoza.
Daga nan ne dai sai jami'in hulda da jama'a da yada labarai na rundunar ya bukaci dukkan al'umma da su cigaba da kai rahoton duk wata maboyar 'yan ta'addan da suka sani.
Haka zakika labarin da muke samu da dumin sa na nuni ne da cewa wasu 'yan bindiga dadi da ba'a san ko suwaye ba sun yi wa wata majami'a a garin Awka na jihar Anambra dirar mikiya inda kuma suka harbe faston cocin.
Kawo zuwa hada wannan labarin dai majiyar mu ta ce ba'a gama tantance ainihin halin da faston yake ciki ba biyo bayan kai shi wani boyayyen wuri da mabiyan sa sukayi.
Ga wasu daga hotunan maboyar nan tasu da kuma mutanen da aka kubutar:

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng