Kwanaki 1000 da tsare El-Zakzaky: ‘Yan Shi’a sun gudanar da zanga-zanga a Abuja

Kwanaki 1000 da tsare El-Zakzaky: ‘Yan Shi’a sun gudanar da zanga-zanga a Abuja

Daruruwan mabiya addinin Shi’a sun gunadar da zanga-zangan lumana domin bukatan sakin shugabansu, Ibrahim El-Zakzaky, wanda yake tsare tun watan Disamban 2015 sakamakon rikici tsakanin mabiyansa da Sojoji.

Yan Shi’a sun fara zanga-zangan ne daga kwaryan birnin tarayya zuwa kasuwar Wuse.

Akalla yan Shi’a 300 ne suka rasa rayukansu a ranan 12 ga watan Disamba 2015 yayinda sukayi fito na fito da Sojoji ta hanyar tare hanya da hana babban hafsan sojin tarayya, Laftanan Janar Tukur Buratai, wucewa. An kashe soja daya ranan.

Gwamnati ta kai karar Sheik El-Zakzaky da matarsa da kuma wasu mabiyansa biyu kara kotu kan laifin kokarin tada tarzoma a kasa. Daga baya aka fara gurfanar da su a kotu.

KU KARANTA: An cika kwana 1000 da Gwamnatin Najeriya ta cafke Zakzaky

Sanadiyar kin sakinsa da gwamnati tayi, mabiyansa suka dukufa suna gudanar da zanga-zanga kulli yaumin a birnin tarayya Abuja da wasu jihohin Arewa.

Har ila yau kuma, Zakzaky na gurfana gaban babban kotun tarayya dake jihar Kaduna.

Kwanaki 1000 da tsare El-Zakzaky: ‘Yan Shi’a sun gudanar da zanga-zanga a Abuja
Kwanaki 1000 da tsare El-Zakzaky: ‘Yan Shi’a sun gudanar da zanga-zanga a Abuja
Asali: Depositphotos

Babban Kotun Tarayya ta bada iznin a saki babban Malamin da Iyalin sa, sai dai har yanzu Gwamnati tayi mursisi ta ki bin umarnin Kotun. Dama dai ana zargin Gwamnatin Buhari da sabawa umarnin Kotu yadda ta ga dama.

Wata Kungiya mai suna Concerned Nigerians ta shirya zanga-zangar da babu Musulmi babu Kirista domin nunawa Gwamnatin kasar rashin amincewan ta da garkame Ibrahim Zakzaky da ake cigaba da yi ba tare da bin ka’ida ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel