Kanin Dankwambo ya fasa komawa APC, ya bayar da dalili

Kanin Dankwambo ya fasa komawa APC, ya bayar da dalili

- Kanin gwamna Hassan Dankambo na jihar Gombe ya janye niyyarsa na barin PDP domin komawa APC

- Buhari Dankwambo wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen yakin zaben gwamna Dankwambo ya ce ya canja ra'ayinsa ne bayan ya yi shawara da 'yan uwa da abokan siyasa

- Buhari Dankwambo ya nuna bacin ransa kan yadda wasu 'yan siyasa ke amfani da batun ficewarsa daga PDP domin haifar da gaba tsakaninsa da yayansa (Gwamna Dankwambo)

Buhari Mohammed Dankwambo, jigo a jam'iyyar PDP a jihar Gombe, kuma kanin gwamna Hassan Dankwambo na jihar Gombe ya canja ra'ayinsa kan batun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC kamar yadda ya fadi a ranar Laraba 5 ga watan Satumban 2018.

Kanin Dankwambo ya janye niyyarsa ta komawa APC
Kanin Dankwambo ya janye niyyarsa ta komawa APC
Asali: Twitter

Mun samo daga Vanguard cewa Buhari Dankwambo ya yanke shawarar cigaba da kasancewa a jam'iyyar PDP ne bayan ya yi shawara da 'yan uwansa da kuma sauran aminansa na siyasa.

DUBA WANNAN: Miji na zargin matar sa da cin amana saboda ya ga kororon roba a jakar ta

A cewar Buhari, "ban ji dadin yadda wasu 'yan siyasa su kayi amfani da matakin da na dauka domin tayar da rikici tsakani na da yaya na (Gwamna Dankwambo).

"Kamar yadda kuka sani, tare da ni akayi gwagwarmayar tabbatar da cewa yayana ya yi nasarar zama gwamna. Ni dan jam'iyyar PDP ne mai biyaya ga jam'iyyar kuma ina biyya ga yaya na gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo.

Kamar yadda kowa ya sani, 'yan adam na iya samun sabani kan wasu batutuwa amma bai dace wasu marasa son zaman lafiya suyi amfani da wannan damar domin jefa gaba tsakanin mu ba.

"Bayan nayi shawara da 'yan uwana da kuma abokan siyasa, na yanke shawarar zan cigaba da zama a PDP."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel