Ranan kin dillanci: 'Yan sanda sunyi ram da wasu 'yan kungiyar asiri 11

Ranan kin dillanci: 'Yan sanda sunyi ram da wasu 'yan kungiyar asiri 11

Asirin wasu matasa 'yan kungiyar asiri na “The New Black Movement of Africa” ya tonu yayin da suke bikin yin maraba da sabon mamba amma ya kasa jure azabar da ake gana masa kafin ya shiga kungiyar.

A jiya, Alhamis ne Jami'an hukumar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Legas suka cafke wasu matasa 'yan kungiyar asiri 11 a Jakande Estate, da ke Ajah a Jihar Legas.

Asirin su ya tonu ne lokacin da daya daga cikin sabbin mambobin kungiyar ya gaza jure duka da azaba da 'yan kungiyar ke gana masa kafin a tabbatar cewa ya cancanta ya shiga kungiyar.

Ranan kin dillanci: 'Yan sanda sunyi ram da wasu 'yan kugiyar asiri 11
Ranan kin dillanci: 'Yan sanda sunyi ram da wasu 'yan kugiyar asiri 11
Asali: Twitter

Ana cikin gana masa azaban ne matashin ya nemi hanya ya tsere zuwa gidan mahaifiyarsa da ke Jakande Estate a Ajah misalin karfe 10 na dare, sai dai ragwancin da ya nuna ya fusata 'yan kungiyar asirin.

DUBA WANNAN: Miji na zargin matar sa da cin amana saboda ya ga kororon roba a jakar ta

Hakan yasa suka bi sahunsa har zuwa unguwar da gidan mahaifiyarsa ya ke inda suka rika dukan duk wanda suka hadu dashi a hanya suna kwace kudaden mutane da wayoyin salula.

Wannan tashin hankalin da mahaifin yaron da ta gani yasa ta zame jiki ta fice daga gidan ta yiwa 'yan sanda Ilasan wayan, nan take CSP Onyinye Onwuamaegbu ya jagoranci tawagar 'yan sanda zuwa gidan inda suka damke 'yan kungiyar asirin 11.

Wadanda aka kama sune, Godwin Victor, Benjamin Daniel, Saviour Anioffiong, Lawal Ibrahim, Shola Odekunle, Sodiq Olawuyi, Segun Fagbohun, Bashiru Lawal, Chinedu Francis, Wahab Adams da Ifarinde Adeniyi.

'Yan sandan sun same su da bindiga kirar Najeriya guda daya, harsashi guda 4, adduna 3, babbar guduma 1, dorinar doki 10 da wasu guraye da laya daban-daban.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel