An dabawa dan takarar shugaban kasar Brazil, Bolsonaro, wuka a ciki ana tsaka da taron gangamin yakin zabe

An dabawa dan takarar shugaban kasar Brazil, Bolsonaro, wuka a ciki ana tsaka da taron gangamin yakin zabe

-Dan takarar shugaban kasar Brazil, Bolsonaro, ya shiga mawuyacin hali bayan da wani ya daba masa wuka a ciki a lokacin da ya ke gangamin yakin zabe

- Likitocin da suka yi masa aiki sun ce yana tsakiyar rai ko mutuwa, amma sun yi masa aikin da zai iya dawo da rayuwarsa

- A watan Mayu, An kashe Marielle Franco, wata jigo a jam'iyyar SFP da ke jagorantar garin Rio de Janeiro, tare da direbanta, Anderson Gomes

Jair Bolsonaro, dan takarar shugaban kasa mafi kwarjini a zaben shugaban kasar Brazil da za'a gudanar a watan gobe, ya shiga mawuyacin hali bayan da wani ya daba masa wuka a ciki a lokacin da ya ke gangamin yakin zabe.

An garzaya da Bolsonaro asibitin garin Juiz de Fora, wanda ya ke mil 125 ga arewacin garin Rio de Janeiro. Masoyan sa ne suka dauke shi a saman kafadunsu, jim kadan da aka ankara da cewar wani ya caka masa wuka.

Bisa rahotannin da aka tattara, ya na cikin mawuyancin hali bisa wannan ciwo da yaji a cikinsa, likitocin da suka yi masa aiki sun ce yana tsakiyar rai ko mutuwa, amma sun yi masa aikin da zai iya dawo da rayuwarsa.

Daga cikin hotuna masu motsi da sandararru da aka rinka yadawa, ya nuna yadda aka cakawa Bolsonaro wuka. Ana iya ganinsa yana daga hannu ga masoyansa, inda a lokaci daya kuma ya rike cikinsa wanda jini ya fara jika rigarsa, tare da yin kara cikin zogi kafin daga bisani ya yanke jiki ya fada a hannun wani da ke bayansa.

An dabawa dan takarar shugaban kasar Brazil wuka a ciki ana tsaka da taron gangamin yakin zabe
An dabawa dan takarar shugaban kasar Brazil wuka a ciki ana tsaka da taron gangamin yakin zabe
Asali: Getty Images

KARANTA WANNAN: 2019: Ararume, Izunaso sun sauya sheka daga APC zuwa APGA

Duk da cewa yana sanye da rigar hana harsashin bindiga wucewa, wukar ta samu nasarar shiga jikinsa ta kasan rigar. Rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa wanda ake zargi da kai harin, mai suna Adelio Bispo de Oliveira ya shiga hannu.

Da wannan rahotanni suka tabbatar da cewa kaiwa yan siyasa hari ya kara karuwa a cikin yan watannin nan. A watan Mayu, An kashe Marielle Franco, wata jigo a jam'iyyar SFP da ke jagorantar garin Rio de Janeiro, tare da direbanta, Anderson Gomes.

Haka zalika a wannan watan, an kai mummunan hari ga jerin gwanon magoya bayan tsohon shugaban kasar Luiz Inacio Lula da Silva, sai dai a lokacin Lula baya cikin tawagar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel