Musulmai sun buƙaci hutun Sabuwar Shekara ta Musulunci

Musulmai sun buƙaci hutun Sabuwar Shekara ta Musulunci

Kamar kullum wasu kungiyoyin musulmai na kasar nan na sake mika buƙatar su tare da yin kira ga gwamnatin tarayya da na jihohi akan su kaddamar da hutun sabuwar shekara ta Musulunci tare da sanya shi cikin dokar kasa.

A yayin da sauran kwanaki kadan sabon watan Musulunci na Muharram ya kama, wasu kungiyoyi na kira ga gwamnatocin kasar nan akan kaddamar da hutun sabuwar shekarar bisa tsari na dokar kasa gami da adalci ga al'ummar Musulmi ta Najeriya.

Kamar yadda shafin jaridar Today Nigeriya ya ruwaito, kungiyoyin da suka bayyana wannan muhimmiyar bukata sun hadar da; kungiyar Musulman 'yan jarida ta Najeriya, kungiyar musulman jami'ar Obafemi Awolowo da kuma ta Musulmai al'ummar jihar Oyo.

Sauran kungiyoyin sun hadar da; kungiyar shawarwari da tuntube-tuntube ta Musulmai, kungiyar musulmai Mata ta Najeriya da kuma kungiyar Musulman Dalibai na Najeriya.

Musulmai sun buƙaci hutun Sabuwar Shekara ta Musulunci
Musulmai sun buƙaci hutun Sabuwar Shekara ta Musulunci
Asali: Twitter

Legit.ng ta fahimci cewa, kungiyoyin sun yi wannan kira ne da sanadin shugabannin su a shiyoyin su daban-daban, inda suke kira ga gwamnatin kasar nan akan ta sake dogon nazari dangane da wannan muhimmin lamari da ya shafi al'ummar Musulmi ta Najeriya.

KARANTA KUMA: An garkame wasu Mutane 2 bisa laifin yiwa karamar Yarinya da wata Mata fyade a jihar Gombe

Kungiyoyin sun yi wannan kira ne akan gwamnatin tarayya ta kaddamar da ranar 1 ga watan farko na Musulunci watau watan Muharram kamar yadda aka saba koda yaushe na kaddamar da 1 ga watan Janairu a matsayin ranar hutu a kasar nan.

Musulmai na duniya baki daya na ci gaba da kiradadon sabuwar shekara ta 1440 bayan Hijirar Fiyayyen Halitta da ka iya kasancewa daidai da ranar 11 ga watan Satumba na shekarar 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel