Tuna-baya: Lokacin da Buhari ya jinjinawa tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso

Tuna-baya: Lokacin da Buhari ya jinjinawa tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso

Wani tsohon bidiyo ya zo hannun mu inda aka ji yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya rika tofawa tsohon Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso albarka a baya inda har ya nemi Allah ya sakawa Gwamnan da alheri.

Tuna-baya: Lokacin da Buhari ya jinjinawa tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso
Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Kwankwaso
Asali: UGC

Magoya bayan Kwankwaso sun tuno da irin yabon da Shugaba Buhari da kan sa ya rika yi wa tsohon Gwamnan na Kano. Shugaba Buhari ya yabawa kokarin da Kwankwaso yayi wajen gina gidaje da kuma tituna da gadoji a Kano.

Bayan nan Shugaba Buhari, ya kuma jinjinawa kokarin da Kwankwaso yayi wajen gyara harkar ilmi a Jihar Kano. Buhari ya yabawa Jami’o’in da Gwamnatin Injiniya Kwankwaso ta gina a lokacin mulkin sa a 1999 da kuma 2011.

KU KARANTA: Wasu shugabannin PDP a Kano sun amince da nadin yaron Kwankwaso

Buhari a wancan lokacin yake cewa duk wanda ya san Jihar Kano, lallai ta canza a lokacin Kwankwaso. Shugaba Buhari ya kara da cewa Injiniya Rabiu Kwankwaso ya nuna tattali wajen rikon Jihar Kano don haka sai dai a yaba masa.

Yanzu dai Sanata Rabiu Musa Kwanwakaso ya fice daga APC ya koma Jam’iyyar PDP inda ya shirya fafatawa a zabe mai zuwa da Shugaba Buhari idan har ya samu tikitin PDP. A 2014 ne Kwankwaso ya bar PDP mai mulki ya koma Jam’iyyar APC.

Ga wani sashen bidiyon nan inda Buhari ya rika yabon Kwankwaso lokacin ana tafiya tare.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel