2019: Kwankwaso ya tattauna da kungiyar kiristocin Najeriya game da takarar shugaban kasa

2019: Kwankwaso ya tattauna da kungiyar kiristocin Najeriya game da takarar shugaban kasa

A yayin da babban zaben shekarar 2019 ke kara karatowa, yan siyasa masu muradin darewa kujeru ko mukamai daban daban na wasa wukarsu, tare da neman goyon bayan jama’a da kungiyoyi da dama.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito tsohon gwamnan jahar Kano kuma dan takara a inuwar jam’iyyar PDP, Sanata Rabius Musa Kwankwaso ya kai ziyara babban ofishin kungiyar kiristocin Najeriya ta kasa, CAN, a ranar Laraba 5 ga watan Satumba.

KU KARANTA: Yaki da cin hanci da rashawa: An fatattaki mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Najeriya

2019: Kwankwaso ya tattauna da kungiyar kiristocin Najeriya game da takarar shugaban kasa
2019: Kwankwaso da CAN
Asali: Twitter

A yayin wannan ziyarar, Kwankwaso ya gana da shugaban kungiyar CAN, Fasto Samson Ayokunle a ofishin kungiyar dake garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Kwankwaso ya daura hotunan ziyarar daya kai ma kungiyar CAN a shafinsa na Twitter, inda yace “Jiya na kai ziyara ga shugaban kungiyar kiristocin Najeriya, Dakta S.O Ayokunle a ofishinsa dake Ibadan.”

A wani labarin kuma rahotanni sun bayyana cewa an yi wata haduwa tsakanin Kwankwaso da Ganduj a yayin wannan ziyarar daya kai inda suka hadu a filin sauka da tashin jirage na jihar Oyo.

2019: Kwankwaso ya tattauna da kungiyar kiristocin Najeriya game da takarar shugaban kasa
Kwankwaso da CAN
Asali: Twitter

Idan dai za’a iya tunawa, yaron gwamnan jihar Oyo, Isiaka Abiola Ajimobi ne ke auran diyar gwamna Abdullahi Umar Ganduje, bikin da mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sunusi II ya daura shi a farkon shekarar 2018.

Don haka ake tunanin mai yiwuwa ne a lokacin da Sanatan Kwankwaso ke hanyarsa ta zuwa ofishin kungiyar kiristocin Najeriya, shi kuwa Gwamna Ganduje wurin surukansa za shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel