Ba zan iya biyan naira miliyan 45 kudin shiga takara ba– Inji dan takarar shuaban kasa a APC

Ba zan iya biyan naira miliyan 45 kudin shiga takara ba– Inji dan takarar shuaban kasa a APC

Wani sabon dan takarar kujerar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar APC, SKC Ogbonnia ya yi watsi da tsarin fidda gwani a takarar shugaban kasa na kato bayan kato da jam’iyyar APC ta yanke shawarar yin amfani da shi, inji rahoton premium times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito SKC ya nuna bacin ransa game da wannan tsarin, har ma yayi barazanar shigar da jam’iyyar kara akan wannan bayu idan har jam’iyyar bata bashi gamsassun bayanai ba da suka sanya su daukar matakin nan ba cikin kwana biyu.

KU KARANTA: Yaki da cin hanci da rashawa: An fatattaki mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Najeriya

Ba zan iya biyan naira miliyan 45 kudin shiga takara ba– Inji dan takarar shuaban kasa a APC
Dr SKC
Asali: Depositphotos

SKC yace ya zama wajibi ya bayyana bacin ransa gay an jaridu, tunda dai shugabancin APC ta kasa taki ta bayyana sauran yan takarkarun shugaban kasa da zasu fafata da Buhari “Ya kamata ace yan jaridu sun yayata sauran yan takarkaun shugaban kasa dake hamayya da Buhari.

“Ko ba komai duniya zata sani cewa akwai wasu yan takarkarun banda Buhari, amma yanzu idan kana karanta jaridu sai kaga kowa akan Buhari kawai yake magana sai kace shi kadai ne dan takara, dimukradiyyarmu ba zata cigaba ba a haka.” Inji shi.

SKC ya cigaba da facdin “Idan da yan jaridu na tattaunawa akan sauran yan takarkarun, da jama’an Buhari sun yi ta kashe kudade, amma kaga yanzu ba zasu kashe ko sisi ba wajen zabe fitar da yan takara saboda yan jaridu sun nuna cewa babu masu takara da Buhari.

“Na aika ma Oshimole da wasika don kada a kuskura ayi amfani da zaben kato bayan kato, saboda na san ta zaben daliget ne kadai za’a ji muryoyinmu, za’a ji muryata za’a ji na Buhari. A yanzu ina jiran martaninsu, idan har basu gamsar da ni cikin kwanaki biyu ba, zan garzaya kotu” Inji shi.

“Na san farashin N45m da aka sanya na shiga takarar shugaban kasa saboda ni aka shi, tabbas b azan iya biyan wannan kudi ba, amma abin tambaya anan shine sauran yan takara zasu iya? Gaskiya nima ba zan biya ba saboda wannan ba dimukradiyya bane.” Inji shi.

Daga karshe SKC yayi kira ga hukumar zabe ta kasa, INEC da ta shirya taron yan takarkarun shuwagabannin kasa kafin jam’iyyiu su fara gudanar da zabukan cikin gida, haka zalika ya caccaki Oshimole saboda rashin gayyatar sauran yan takarkarun zuwa taron majalisar koli na APC.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel