Shugabannin PDP a Kano sun yi wa sabon Shugaban rikon kwarya Rabiu Bichi mubaya’a

Shugabannin PDP a Kano sun yi wa sabon Shugaban rikon kwarya Rabiu Bichi mubaya’a

Mun samu labari cewa shugabannin Jam’iyyar PDP na wasu kananan Hukumomi sun yi mubaya’a ga sabon Shugaban PDP na Jihar Dr. Rabiu Sulaiman Bichi wanda Uwar Jam’iyya ta nada kwanan nan.

Shugabannin PDP a Kano sun yi wa sabon Shugaban rikon kwarya Rabiu Bichi mubaya’a
Shugabannin PDP a Ribas tare da Kwankwaso da mutanen sa
Asali: Twitter

Babban Hadimin wani tsohon Kwamishinan Jihar Kano Abdullahi Sani Rogo watau Muhammadu Bashir Amin ya bayyana cewa wasu Shugabannin PDP a Kananan Hukumomi sun goyi bayan matakin da Jam’iyyar PDP ta dauka.

A baya nan ne PDP ta rushe shugabancin ta a Kano ta nada kwamitin rikon kwarya. Hakan ne kusan dalilin da ya sa irin su tsohon Gwamnan Jihar watau Malam Ibrahim Shekarau su ka kama hanyar ficewa daga Jam’iyyar zuwa APC.

KU KARANTA: Wani babban Sarki ya tsinewa masu barin PDP zuwa APC

Bashir Amin ya rahoto cewa wasu shugabannin PDP na Kananan Hukumomi na Tarauni, Kumbotso, Kano Municipal da kuma Ungogo sun ziyarci sabon shugaban da aka nada na rikon kwarya a gidan sa inda su ka jadadda mubaya’ar su.

Wadannan shugabannin dai su ne Murtala Musa, Ahmad Dada, Sagir Shelling da kuma Malam Da Asabe. PDP ta rusa shugabanci Jam’iyyar ne domin a tafi da wasu manyan mukarraban tsohon Gwamna Kwankwaso da su ka bar APC kwanaki.

Dazu kun samu labari cewa ‘Dan takarar Shugaban kasa Rabiu Kwankwaso ya cika fam din sa na tsayawa a zaben 2019 ya maidawa Hedikwatar Jam’iyyar PDP na kasa kamar yadda doka ta tanada.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel