Wasu ‘Yan siyasan Kaduna sun sha ban-ban da El-Rufai wajen fitar da gwanayen APC

Wasu ‘Yan siyasan Kaduna sun sha ban-ban da El-Rufai wajen fitar da gwanayen APC

Sanatan Kaduna ta tsakiya watau Shehu Sani da wasu ‘Yan Majalisan APC da masu neman kujerar Majalisa sun sha ban-ban da wasu manyan Jam’iyyar APC a Kaduna inda su ka nemi a canza tsarin tsaida ‘Yan takaran Jam'iyya.

Wasu ‘Yan siyasan Kaduna sun sha ban-ban da El-Rufai wajen fitar da gwanayen APC
Shehu Sani ya sha ban-ban da Gwamna El-Rufai a Kaduna
Asali: Depositphotos

Sani ya sake sukar Jam’iyyar APC na shirin da ta ke yi na gudanar da zaben fitar da gwani inda yace tsarin da za ayi amfani da shi zai yi sanadiyyar amfani da kudi da karfin iko wajen zaben wanda Jam’iyya za ta ba tuta.

Sanatan ya nuna cewa bai dace ace Gwamnatin Buhari ta na yaki da rashin gaskiya amma ace Jam’iyyar APC ta dauki hanyar da babu gaskiya ciki wajen tsaida wanda za su rike mata tuta a zabe mai zuwa na 2019 ba.

‘Dan Majalisar ya yabi matakin da APC ta dauka a Jihohi irin su Kano da Neja na yin amfani da zaben kato-bayan-kato wajen tsaida ‘Yan takaran ta. Jihohin APC da dama dai su na kukan cewa ba za su iya bin wannan tsari ba.

KU KARANTA: An sayawa Buhari fam din tsayawa takara a APC

Da alamu dai Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ba zai so ayi amfani da zaben kato-bayan-kato wajen fitar da ‘Yan takarar Majalisa a Jihar ba. Dalilin haka ne wasu manya a APC ta Jihar Kaduna su ka nemi uwar Jam’iyya ta sa baki.

Mohammed Sani, Aliyu Silver, Shamsuddeen Shehu, Honarabul Rufai Chanchangi, Mohammed Musa, Halal Falal, Usman Ibrahim sun aikawa Hedikwatar APC na kasa wasika su na mai nema ayi amfani da ‘yar tinke a zaben bana.

Jiya kun ji cewa wasu Matasa da ke goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari sun yi zanga-zanga a babban ofishin Jam’iyyar APC kwanan nan su na masu kira ayi amfani da zaben ‘yar tinke wajen zaben ‘Yan takarar Jam’iyyar a zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel