Shugaba Buhari da Mataimakin sa sun yi sabani kan batun 'Yan sanda jiha

Shugaba Buhari da Mataimakin sa sun yi sabani kan batun 'Yan sanda jiha

Da sanadin shafin jaridar Premium Times mun samu cewa, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana rashin amincewar sa karara da shugaban kasa Muhammadu Buhari, dangane da batun samar da 'yan sandan jihohi a kasar nan.

Osinbajo da shugaba Buhari sun hau shafi daban-daban kan batun danka iko da mallakin gudanarwar 'yan sanda a hannun gwamnatocin jihohi kamar yadda ake ta kwan-kwashe daga wasu lunguna da sako na kasar nan ta bayyana wannan bukata.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, tun da dadewa ya kasance yana goyon bayan mai she da ikon gudanarwar 'yan sanda a hannun gwamnatoci jihohi na kasar nan sakamakon rashin tasirin inganci da nagartar su a hannun gwamnatin tarayya.

Shugaba Buhari da Mataimakin sa sun yi sabani kan batun 'Yan sanda jiha
Shugaba Buhari da Mataimakin sa sun yi sabani kan batun 'Yan sanda jiha
Asali: Depositphotos

Mataimakin shugaban kasar dai ya bayyana hakan ne a yayin mayar da martani ga tsohon shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, dangane da sukar gwamnatin su yayin bayyana tsare-tsaren sa na shugabanci dangane da yakin neman zaben kujerar shugaban kasa da ya kafa kahon zuka a kai.

Legit.ng ta fahimci cewa, a sanadiyar wannan muhawara ce mataimakin shugaban kasar ya bayyana sashen da ya yi sabani da shugaba Buhari tare da nesanta kansa dangane da wannan batu na 'yan sandan jihohi da ya kasance wani bigire cikin tsare-tsare na sauya fasalin kasa.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa, shugaba Buhari yana nan akan bakansa na rashin amincewa da 'yan sandan jihohi inda ya bayar da dalilin sa na cewa, ba bu wadataccen tattalin arziki a jihohin kasar nan da za su iya mallakar 'yan sandan na karan kansu.

KARANTA KUMA: Kudaden Shiga: Hukumar Kastam ta samar da N140bn a watan Agusta

Cikin zayyana dalilansa shugaba Buhari ya bayyana cewa, rashin wadataccen arziki ta bangaren gwamnatocin jihohi da a wani sa'ilin suke gazawa wajen biyan albashin ma'aikatan su akan kari ya sanya wannan lamari ba zai tabbata ba cikin kasar nan a halin yanzu.

Ya ke cewa, "ba zai yiwu a horas da mutum tare da mallaka ma sa makamaki kuma a gaza biyansa albashi lokacin da ya dace ba, ko shakka babu akwai barazana a wannan lamari" kamar yadda ya bayyana yayin ganawarsa da kafar watsa labarai ta Muryar Amurka a watan Mayun da ya gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel