Wasu na hannun daman 'yan takaran shugabancin kasa 2 a PDP za su koma APC

Wasu na hannun daman 'yan takaran shugabancin kasa 2 a PDP za su koma APC

Mun samu daga Leadership cewa Buhari Mohammed Dankwambo, kani ga gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo da Auwal Abdullahi Gafakan Akko, jagoran yakin neman zaben shugabancin kasa na Sanata Ahmed Makarfi suna shirin ficewa daga PDP so koma APC.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa mutanen biyo suna da magoya baya sosai musamman cikin matasan jihar Gombe da kewaye kuma zasu tattara dubban magoya bayansu su koma APC.

A yau Laraba, Ibrahim Hassan Dankwambo, wanda akafi sani da MBD ya tabbatarwa manema labarai a Gombe cewa ya kammala shiri tsaf na komawa APC, inda ya kara da cewa ya jinkirta ne saboda wasu masu ruwa da tsaki a APC sun bukaci ya dakata a shirya masa babban liyafa na tarbarsu.

Wasu na hannun daman 'yan takaran shugabancin kasa 2 a PDP za su koma APC
Wasu na hannun daman 'yan takaran shugabancin kasa 2 a PDP za su koma APC
Asali: Twitter

"Zamu sanar da mutane da zarar mun kammala shirye-shiryen mu da masu ruwa da tsaki a APC," inji Dankwambo.

DUBA WANNAN: Birkice gidan Clark: An kama dan tsurkun da ya yiwa 'yan sanda ingiza mai kantu

Kazalika, wata majiya kwakwara ta ruwaito cewa BMD ya taka muhimmiyar ruwa wajen nasarar yayansa a zaben gwamna na 2015 a jihar Gombe.

Bayan BMD, wani sananen 'dan siyasa a Gombe, kuma jagoran yakin neman zaben shugabancin kasa na Sanata Makarfi, Auwal Abubakar, yana shirin ficewa daga PDP ya koma APC.

Tsohon sakataren PDP a yankin Pindiga, Adamu Mamman shima yana shirin ficewa daga PDP tare da Auwal.

"Na yanke shawarar komawa APC ne saboda irin yaudarar da gwamna Dankwambo ya ke mana, ina son in shiga APC saboda in bayar da gudunmawa ta wajen cigaban jama'an yanki na." inji Auwal.

A hirar da ya yi da Leadership, Mamman ya ce ficewar wadannan mutanen babban asara ce ga jam'iyyar PDP. Ya kara da cewa zasu kara wa jam'iyyar APC farin jini da jama'a.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164