Da dumi-dumi: Yan Boko Haram sun sace yan mata a Borno

Da dumi-dumi: Yan Boko Haram sun sace yan mata a Borno

- Kwana biyu bayan hari kan sojoji, yan Boko Haram sun sace mata

- Sun tare motocin matafiya a karamar hukumar Gwoza

Yan kungiyar tada kayar baya ta Boko Haram sun yi garkuwa da wasu yan mata a hanya Pulka dake karamar hukumar Gwoza na jihar Borno a jiya Talata.

Matan na kan hayan tafiya zuwa wata karamar hukuma da ke makwabtakansu ne yan Boko Haram suka tare su.

Daya daga cikin fasinjojin mota mai suna, Muhammad Buba, ya bayyanawa manema labarai cewa mutane da yawa sun jikkata yayinda suke kokarin tsira daga wannan hari.

Buba bai fadi ko an kashe wani ba amma ya ce sun ji ruwan harsasai ne daga wurare daban-daban.

Da dumi-dumi: Yan Boko Haram sun sace yan mata a Borno
Da dumi-dumi: Yan Boko Haram sun sace yan mata a Borno
Asali: UGC

Idrissa Hamisu, wani fasinjan motan ya kara da cewa yan Boko Haramun zun hau motoci biyu kirar Toyota Hilux

“Da yawa daga cikin wadanda suka sace mata ne marasa karfin guduwa. Wannan abu ya faru ranan Talata,”

“Ban sani ko jami’an sojin sun samu nasarar ceto fasinjojin ba amma an sace mata da yawa a harin”

KU KARANTA: Miji da mata sun sayar da yaronsu daya tilo N180,000 a garin Calabar

Jaridar The Cable ta yi kokarin magana da kakakin hukumar soji, Texas Chukwu, akan wannan al’amari amma ba’a sameshi a way aba.

Wannan hari ya faru ne kwana biyu bayan an kaiwa sojoji hari har barikinsu a jihar Borno.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel