Nan gaba kadan za'a fara ginin Jami'ar sufuri a garin Daura, jihar Katsina - Amaechi

Nan gaba kadan za'a fara ginin Jami'ar sufuri a garin Daura, jihar Katsina - Amaechi

- Mr. Rotimi Amaechi, Ministan zirga zirga, ya ce nan da farkon shekarar 2019 za'a fara ginin jami'ar sufuri a garin Daura, jihar Katsina

- Ministan ya bayyana cewa kamfanin "China Civil and Construction Company (CCECC)", shi ne zai gudanar da aikin gina jami'ar

- Amaechi ya ce da zaran gwamnatin jihar ta bayar da filin, kamfanin CCECC zai isa filin, ya kewaye shi don fara aikin ginin

Ministan zirga zirga, Mr. Rotimi Amaechi, ya ce nan da farkon shekara mai zuwa za'a fara ginin jami'ar sufuri a garin Daura, jihar Katsina, wacce za'a kashewa kudi Naira Biliyan 18.

Kamfanin "China Civil and Construction Company (CCECC)", shi ne zai gudanar da aikin gina jami'ar, wanda hakan na daga cikin yunkuri na gwamnatin tarayya na samar da kwararru da zasu kula da mafi yawan gine ginen sufuri da na layin dogo da ke a fadin kasar.

Ministan ya shaidawa manema labarai a Abuja, cewa bayan jihar Katsina, akwai yiyuwar gina wata jami'ar sufuri a jihar Rivers, don samar da kwararru da za su magance matsalolin sufuri da ake fuskanta a kasar.

KARANTA WANNAN: A cikin shekaru 2 zan farfado da tattalin arzikin Nigeria idan aka zabe ni a 2019 - David Mark

Nan gaba kadan za'a fara ginin Jami'ar sufuri a garin Daura, jihar Katsina - Amaechi
Nan gaba kadan za'a fara ginin Jami'ar sufuri a garin Daura, jihar Katsina - Amaechi
Asali: Facebook

Ya ce tuni an baiwa kamfanin CCECC kwangilar gina jami'ar, wacce ake sa ran fara aikin da zaran gwamnan jihar ya bayar da filin da za'ayi ginin, yana mai karawa da cewa da zaran gwamnatin jihar ta bayar da filin, kamfanin CCECC zai isa filin, ya kewaye shi don fara aikin ginin.

Amaechi ya ce matasan Nigeria da ake horas da su a kasar Sin akan fasahar jiragen kasa, bayan kammala horonsu, za'a basu guraben ayyukan koyarwa a wadannan jami'o'i na wani lokaci, kafin daga bisani a barsu suyi ayyuka a wuraren da suke bukata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel