2019 tuwona maina: Surukin Buhari, Modi ya shiga takarar gwamnan jahar Adamawa

2019 tuwona maina: Surukin Buhari, Modi ya shiga takarar gwamnan jahar Adamawa

Surukin Buhari, watau kanin uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha, mai suna Modi ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jahar Adamawa a zaben shekarar 2019, inji rahoton Sahara.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Modi, wanda cikakken sunansa Dakta Mahmoud Halilu Ahmed ya bayyana bukatartasa ta taka takarar mukamin gwamnan jihar Adamawa ne cikin wasikar daya aika ma shugaban jam’iyyar APC reshen jahar Adamawa.

KU KARANTA: Najeriya, UN da wasu manyan kasashe 2 zasu lalubo hanyar kawo karshen Boko Haram a Turai

2019 tuwona maina: Surukin Buhari, Modi ya shiga takarar gwamnan jahar Adamawa
Alhaji Modi (Daga hagu)
Asali: Depositphotos

A cikin wannan budaddiyar wasika da Modi ya aika ma shugaban APC, yace “Ina shirin kaddamar da takarata ta neman mukamin gwamnan jihar Adamawa a ranar 10 ga watan Satumba da misalin karfe 12 a garin Yola.

“Biyo bayan bukatar jam’iyyarmu na fadada farfajiyar siyasa don jama’a da dama su fafata, tare da samar da yanayi mai aminci ga kowa, ina sanar da kai niyyata ta neman mukamin gwamnan jahar Adamawa a zaben 2019 cikin jam’iyyar APC.” Inji shi.

Modi ya kara da cewa bukatarsa ta tsaywa takarar gwamna ya faru ne sakamakon kishin kasa dake tattarare da shi, da kuma burin magance matsalolin dake fuskantar jahar, har ma da inganta walwalar al’ummar jahar.

Majiyarmu ta bayyana cewa takarar gwamna da Modi ya fito baya rasa nasaba da tsarin zaben kato bayan kato da shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomole ya kawo, don kawo karshen yadda gwamnoni ke matse jam’iyya a hannunsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel