Jarumin maza: Wani Soja ya mutu yayin da yake kokarin ceto wata Mata daga ambaliyan ruwa

Jarumin maza: Wani Soja ya mutu yayin da yake kokarin ceto wata Mata daga ambaliyan ruwa

Kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta ruwaito an gano gawar wani jarumin Soja daya gamu da ajalinsa a lokacin dayake kokarin wata mata daga ambaliyar ruwa a jihar Kebbi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sojan mai suna Marcell Nwanko yana da mukamin Warrant Officer a rundunar Sojan kasa ta Najeriya, yana tare ne da runduna ta 223 na Sojan Najeriya dake Zuru jahar Kebbi.

KU KARANTA: Najeriya, UN da wasu manyan kasashe 2 zasu lalubo hanyar kawo karshen Boko Haram a Turai

Wannan lamari mai muni ya faru ne a ranar 30 ga watan Agusta inda ambaliyan ruwa ya shafi kauyen Kanya dake cikin karamar hukumar Wasagu, da kauyen Mahuta dake cikin karamar hukumar Fakai, wanda yayi sanadin asarar rayukan mutane tara da dukiyoyi da dama.

Jarumin maza: Wani Soja ya mutu yayin da yake kokarin ceto wata Mata daga ambaliyan ruwa
Ambaliyan ruwa
Asali: Facebook

Majiyarmu ta ruwaito Soja Nwanko yana kokarin ceto wata mata ne daga ambaliyan, amma hakan bai yiwu ba, inda ruwan ya halak matar, kuma ya halaka Sojan, amma an samu gawar matar a ranar, shi kwau Sojan sai a yau aka gano gawarsa a kauyen Unashi cikin karamar hukumar Wasagu.

Kaakkain gwamnan jahar Kebbi, Abubakar Dakingari ya sanar da cewa an gano sauran gawarwakin mutane biyar a kauyen Kanya, yayinda sauran gawarwaki biyu kuma aka ganosu a kauyen Mahuta.

Dakacin kauyen Kanya, Alhaji Isah Dan Hassan ya roki gwamnan jihar Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu daya taimakesu, sakamakon ruwa yayi barna ga dabbobinsu, abincinsu, gonakinsu da kuma gidajensu.

Shima shugaban karamar hukumar Fakai, Musa Jarma ya bayyana cewa akalla gidaje 48 ne ambaliyan ta lalata, tare da wata babbar gada data hada sauran yankunan garin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel