Jami’in dan sanda a jihar Legas ya mutu yana zina a cikin ofishinsa

Jami’in dan sanda a jihar Legas ya mutu yana zina a cikin ofishinsa

- Wani jami'an dan sanda ya yi mumunan karshe

- Ya mutu zigidir kan matar aure cikin ofishinsa

- Abokan aikinsa sun bayyana cewa halinsa kenan

Wani Sufritanda na hukumar yan sandan Najeriya a jihar Legas, ya mutu yana zina da wata mata a cikin ofishinsa da ke kwalegin hukumar yan sanda, Ikeja.

Matar, wacce ita kanta matar aure ce, an tsareta a ofishin hukumar yan sandan garin Ikeja, duk da cewa ta musanta zargin cewa ita ta kasheshi.

Game da cewarta, dan sandan mai suna Sunday ya kasance yana amfani da magungunan kara kwazon namijin wajen jama’I duk lokacin da zasuyi lalata.

KU KARANTA: Mummunar dabi'ar Luwadi da Madigo na durkusar da ci gaban Nigeria

Tace: “Ya kasance yana kwanciya da ni a ofishinsa. Ya yi sawu daya amma kamar yadda ya saba, bai isheshi ba.

“Na fada masa a ranan cewa magungunan da yake amfani da su koda yaushe na da illa ga jikina. Bana son abun saboda ni abin yake shafa. Yana kan saduwa da ni sai na ga jikinshi ya canza, kafin in farga kumfa ya fara fitowa daga bakinsa.”

Idanuwan shaida sun bayyana cewa kafin a kawo masa agaji, ya mutu.

An sameshi zindir haihuwar mahaifiyarsa da rigansa kan teburinsa.

Wasu abokan aikinsa sun bayyana cewa ya kasance yana irin wannan abu a cikin ofishinsa tare da mata daban-daban.

Kana tu tuhumcesa da cewa ya kasance yana tilasta yan mata yan sanda wajen kwanciya da shi a ofishinsa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel