Sake fasalin kasa: Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya yiwa Atiku wankin babban bargo

Sake fasalin kasa: Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya yiwa Atiku wankin babban bargo

- Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce sake fasalin kasar kamar yadda Atiku ya bukata ba shine hanyar daga tattalin arzikin kasar ba

- Farfesa Osinbajo ya bayyana hakan a cikin wata wasika da ya aikawa jaridar PremiumTimes, yana mai cewa Atiku yayi hakan don neman tagomashin siyasa

- Idan ba a manta ba, Atiku ya ce hanya mafi sauki na samun nasara wajen sake fasalin kasar shine rage karfin ikon da aka baiwa gwamnatin tarayya

Mataimakin shugaba kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a ranar talatar nan ya maida martani ga tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma mai neman tsayawa takarar shugabancin kasar, Alhaji Atiku Abubakar, da cewar akwai sarkakiya a cikin hanyoyin da Atiku ya kawo na gyara fasalin kasar, kuma hakan hanyar murkushe tattalin arzikin kasar ne.

Osinbajo wanda ya bayyana hakan a cikin wasikar da ya aikawa kamfanin jarida na PremiumTimes, ya yi ikirarin cewa Atiku kawai na son samun tagomashi a siyasance, ta hanyar kawo wasu hanyoyin sake fasalin kasar da shi kansa ba zai iya binsu ba.

Barranta da wannan mataki na Atiku,Osinbajo ya ce: "Ban yarda da cewar wai sake fasalin da kasar take a ciki shine hanya daya 'Jal' da zata warware dukkanin matsalolin tattalin arzikin da kasar take fama da su ba. Yana mai cewa hakan kawai zai hadda batar da kudaden kasar. Sai dai babu musu akan cewa akwai bukatar samar da shugabanci nagari"

Sake fasalin kasa: Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya yiwa Atiku wankin babban bargo
Sake fasalin kasa: Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya yiwa Atiku wankin babban bargo
Asali: Depositphotos

KARANTA WANNAN: Yawan barazanar da APC take yi ba zai bata nasara a jihar Kwara ba - PDP

A cikin wasikar da ya aika, ya ce babu ja, akan cewa yan Nigeria na bukatar shugabanci nagari, alkinta dukiyar kasar kamar yadda ya dace, shayar da yan Nigeria romon demokaradiyya, samar da sahihan hanyoyin ci gaba da dai-daita fasalin kasar kamar yadda Atiku ya bukata.

A baya Legit.ng ta ruwaito cewa a ranar laraba 20 ga watan Yuli, tsohon shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce hanya mafi sauki da saurin samun nasara wajen sake fasalin kasar shine rage karfin ikon da aka baiwa gwamnatin tarayya, tare da maido wasu bangarorin ikon ga gwamnatin jihohi.

Ya ce: "Tsarin baiwa gwamnatin tarayya iko akan jihohi, kungiyoyin sa kai, makarantu da asibitoci, da aka fara tun shekara ta 1970, tsari ne da ya kamata a sake fasalinsa."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel