Yanzu-yanzu: David Mark ya alanta niyyar takara kujeran shugaban kasa a 2019
Tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, ta bayyana cewa gob Talata, 4 ga watan Agusta zai sayi takardan takarar zaben kujeran shugaban kasa a 2019 karkashin jam’iyyar PDP.
An tattaro cewa Sanata David Mark wanda aka fi sani da :Okpokpowulu K’Idoma” zai tsaya takara da sauran masu neman kujeran shugaban kaan guda goma sha biyu.
Domin tabbatar da wannan labari a yau Litinin, shugaban kungoyar masoya David Mark, James Oche, yace bayan yawon neman shawara da sanatan yayi, ya yanke shawaran takara domin ceto Najeriya.

Source: Depositphotos
“Haka, mai yi ya zi. Ya sayi takardar takara rananTalata. Lokacin ceto Najeriya daga rushewa yayi, “ Mr Oche yace.
Sauran yan takaran kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP sune:
Sanata Ahmed Makarfi
Sanata Bukola Saraki
Tanimu Turaki
Jonah Jang
Sule Lamido
KU KARANTA: Gwamnatin kasar Malaysia ta bulale yan mata biyu masu madugo
Aminu Waziri Tambuwl
Attahiru Bafarawa
Malam Ibrahim Shekarau
Ibrahim Dankwambo
Datti Baba Ahmed
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng