2019: Sai mun tika Buhari da kasa - Mata 6 dake takarar shugaban kasa

2019: Sai mun tika Buhari da kasa - Mata 6 dake takarar shugaban kasa

Wasu mata guda 6 dake takarar kujerar shugaban kasa sun bayyana dalilinsu na son karbar mulkin Najeriya daga shugaba Buhari.

Matan 6 – Farfesa Olufunmilayo Adesanya-Davis, Dakta Oluremi Comfort Sonaiya, Dakta Elishama Rosemary Ideh, Adeline Iwuagwu-Emihe, Eunice Atuejide da Princess Oyenike Roberts – sun bukaci masu zabe su bawa mace dama domin kawo canji nan gaskiya a Najeriya.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewar matan na wakiltar kasha 60% na dukkan ‘yan takarar dake burin ganin sun karbi mulkin Najeriya daga hannun shugaba Buhari a zaben 2019.

2019: Sai mun tika Buhari da kasa - Mata 6 dake takarar shugaban kasa
Buhari
Asali: UGC

‘Yan takarar sun kafe kan cewar muddin ‘yan Najeriya na burin ganin canji a rayuwarsu da yadda ake tafiyar da al’amuran gwamnati to su zabi mace a zaben 2019.

Daya daga cikin ‘yan takarar, Rosemary Ideh, dake takara a karkashin jam’iyyar ANN ta ce tana da yakinin kayar da shugaba Buhari a zaben shekarar 2019.

DUBA WANNAN: Rahoto ya bankado dalilin rushewar Cocin Najeriya da aka gina shekara 100 da suka wuce

Wata ‘yar takarar, Adeline Iwuangwu-Emihe, ta bayyana cewar tuni ta ware wasu kudiri 10 da zata kaddamar domin kawo wa Najeriya cigaba da zarar an zabe ta.

A cikin satin da ya gabata ne tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bawa ‘yan Najeriya mamaki bayan ya zubar da hawaye yayin da ya je karbar takardar takarar neman tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP.

Batun zubar da hawayen da Atikun ya yi ta jawo barkewar cece-kuce da tofa albarkacin baki daga ‘yan Najeriya, musamman a dandalin sada zumunta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel