Gwamnatin kasar Malaysia ta bulale yan mata biyu masu madugo

Gwamnatin kasar Malaysia ta bulale yan mata biyu masu madugo

An bulale yan mata biyu a ranan Litinin bisa ga laifin madugo wanda ya sabawa dokokin addinin Musulunci, wannan abu ya janyo cece-kuce daga yank are hakkin dan Adam.

Yan matan, sanye da fararen kaya da mayafansu sun sha bulala shida-shida a wata kotun Shari’a a kasar Malaysia.

Yan yakin kare hakkin dan Adam sunce wannan shine karo na farko da za’a zane mutane domin saba shari’ar Musulunci wanda ya hana auren jinsi. Sunce wannan na kara baiwa mutane masu son yin auren jinsi daya a kasar.

An kafa kasar Malaysia ne akan dokokin biyu. Kotunan shari’a za su iya yanke hukunci kan harkokin addini da iyalan Musulman kasar. Abubuwa irinsu zina da sauransu.

KU KARANTA: An kama mu ne saboda Allah ya kaddara – Yan fashi

Yan matan masu shekara 22 da 32 sun shiga hannun hukuma ne a watan Afrilu bayan an damkesu cikin mota a jihar Terengganu.

Wadannan yan matan da aka sakaye sunayensu sun yi na’am da zargin da ake musu na saba dokan addinin Musulunci kuma na yanke musu hukuncin bulala da taran 3,300 ringgit ($800).

An musu bulala a kotun Shari’a jihar da ke Kuala Terengganu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel