Zaben 2019: Na yi shekaru fiye da 40 ina siyasa a Najeriya – Tsohon Gwamna Bafarawa

Zaben 2019: Na yi shekaru fiye da 40 ina siyasa a Najeriya – Tsohon Gwamna Bafarawa

Mun samu labari cewa tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Attahiru Dalhatu Bafarawa ya bayyana dalilin da ya sa yake neman mulkin kasar nan a karkashin tutar Jam’iyyar adawa ta PDP a 2019.

Zaben 2019: Na yi shekaru fiye da 40 ina siyasa a Najeriya – Tsohon Gwamna Bafarawa
Bafarawa ya bayyana abin da ya sa yake neman mulkin Najeriya
Asali: Depositphotos

Attahiru Dalhatu Bafarawa yayi hira da Daily Trust inda ya bayyana cewa duk da yawan ‘Yan takarar da ke neman Shugaban kasa a PDP, abin ba ya razana sa. Tsohon Gwamnan yace ba ya jin cewa kuma masu neman kujerar a PDP sun yi yawa.

Bafarawa ya bayyana cewa tun 1976 ya shigo siyasa inda aka zabe sa a matsayin Mataimakin Shgaban karamar Hukuma har ta kai ya zama Shugaban Jam’iyyar NRC a tsohuwar Jihar Sokoto. Bafarawa yace su ne kuma su ka kafa UNCP a 1993.

Tsohon ‘Dan siyasar yana kuma cikin wadanda su ka kafa APP wanda ta zama Jam’iyyar ANPP bayan dawowar farar hula don haka yake ganin cewa babu wanda zai nuna masa sanin harkar siyasa cikin masu neman kujerar Shugaban kasa a PDP.

KU KARANTA: 2019

Alhaji Bafarawa yace a lokacin yana Shugaban Jam’iyyar APP na rikon kwarya ne aka fara ba Buhari tikitin takarar Shugaban kasa a 2003. Sai dai tsohon Gwamnan yana ganin cewa Buhari ba zai taba iya mulki ba saboda tsohon Soja ne ba ‘Dan siyasa ba.

Tsohon Gwamna dai yana ganin cewa taron da aka yi kwanaki na tarbar Sanata Aliyu Wammako duk na banza ne. Bafarawa ne ya fara kawo Wammako siyasa a matsayin Mataimakin sa inda yace kuma Gwamna Tambuwal ‘dalibin sa ne a siyasa tun 2003.

Tsohon Gwaman wanda ya bar APC a 2014 ya dawo PDP yana sa ran mulkin Kasar nan inda yake cewa ba a bukatar tsohon Soja ya rika jan ragamar Najeriya. A baya, Bafarawa yayi takarar Shugaban kasa a Jam’iyyun adawa irin su DPP amma bai yi nasara ba.

Tsohon Gwamnan na Sokoto yana cikin masu neman takarar Shugaban kasa a PDP a zaben 2019. Sai dai za a iya gamuwa da rikici a Jihar Sokoto bayan Gwamnan Jihar Aminu Tambuwal ya bar APC ya dawo PDP kuma yana harin kujerar ta Shugaban kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel