‘Yan takaran Shugaban kasa a PDP sun zauna teburi guda wajen bikin Makarfi

‘Yan takaran Shugaban kasa a PDP sun zauna teburi guda wajen bikin Makarfi

Mun samu labari cewa a karshen makon nan, manyan ‘Yan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar adawa ta PDP sun hadu wajen wani daurin aure da aka yi a cikin Garin Kaduna.

‘Yan takaran Shugaban kasa a PDP sun zauna teburi guda wajen bikin Makarfi
Kwankwaso da Sanata Ahmad Makarfi wajen daurin auren yaron sa a Kaduna
Asali: Facebook

A Ranar Asabar ne aka daura auren wani ‘Dan tsohon Gwamnan Kaduna Sanata Ahmad Muhammad Makarfi. Tsohon Gwamnan dai yana cikin masu neman mulkin Kasar nan a karkashin lemar Jam’iyyar adawa PDP a 2019.

Manyan ‘Yan PDP musamman masu neman takarar Shugaban kasar sun halarci wannan babban daurin aure a Garin Kaduna. Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar yana cikin ‘Yan sahun gaba a wajen daurin auren.

Bayan nan kuma tsohon Gwamnan Jigawa sule Lamido yana cikin manyan baki a wajen wannan daurin aure da aka yi. An hangi tsohon Gwamnan tare da Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar su na zantawa.

KU KARANTA: Ba zan bar PDP ba ko da na fadi zaben 2019 - Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso shi ma yana cikin wadanda su ka hau jirgi daga Babban Birnin Tarayya Abuja wajen wannan daurin aure a Kaduna. Sanatan ya hadu da Magajin sa Malam Ibrahim Shekarau a taron.

Bayan nan kuma Gwamnan Jihar Gombe Dr. Ibrahim Hassan Dankwambo yana cikin wanda su ka halarci bikin. Dankwambo wanda ya ke neman Shugaban kasa ya bayyana cewa ya halarci daurin auren a shafin sa na Tuwita.

Kwanaki kun ji cewa Sule Lamido wanda yana cikin ‘Yan gaba-gaba na sahun ‘Yan takarar Shugaban kasar ya leka Jihar Bauchi inda ya nemi mutanen Jihar Bauchi su marawa duk wanda PDP ta tsaida takara baya a zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel