Kabilar Igbo zata zabi Buhari a 2019 don kaucewa kuskurenta na 2015

Kabilar Igbo zata zabi Buhari a 2019 don kaucewa kuskurenta na 2015

- Kungiyar G-23 ta ce kabilar Igbo ba zata sake tafka babban kuskuren da ta yi a zaben 2015 ba, in da ta zabi siyasar kabilanci akan cancanta

- Shugaban kungiyar na shiyyar Kudu maso Gabas, Onunkwo, ya bayyana hakan ga manema labarai a jihar Ribers

- Kungiyar ta kuma yi alkawarin yin aiki kafada da kafada da shugaban kasa Muhammadu Buhari a sake zabensa 2019 a Kudu maso Gabashin kasar

Kungiyar dake kare muradun shugaban kasa Muhammadu Buhari, G-23, ta ce kabilar Igbo ba zata sake yin dambarwar da tayi a zaben 2015 ba, inda ta zabi yin siyasar kabilanci mai maikon zaben cancanta, kamar dai yadda ta zabi tsohon shugaban kasa Jonathan kawai saboda bangarancin shiyya.

Kungiyar ta nuna nadamar abubuwan da suka faru a wancan lokacin, da suka shafi gurguncewar siyasar Kudu maso Gabashin kasar, inda ta ce kabilar Igbo zasu fito kwansu da kwarkwatarsu don marawa Buhari baya, na yin tazarce a zaben 2019.

Shugaban kungiyar G-23 a Kudu maso Gabas, Johnbosco Onunkwo, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Fatakwal, jihar Rivers, a ranar asabar, ya ce gwamnatin shugaban kasa Buhari ta bunkasa yankin Kudu maso Gabas dama kasar baki daya, wanda ala tilas ne a sake bata wata damar.

Kabilar Igbo zata zabi Buhari a 2019 don kaucewa kuskurenta na 2015
Kabilar Igbo zata zabi Buhari a 2019 don kaucewa kuskurenta na 2015
Asali: Depositphotos

KARANTA WANNAN: Shuwagabannin duniya na jerin gwano don ganawa da Buhari duk da Trump ya kirashi 'maras tagomashi

Onunkwo ya kara da cewa gwamnatin Buhari na kokarin aiwatar da ayyukan hanyoyi da gadoji akalla 69 a yankin na Kudu maso Gabas, da suka hada da ginin gadar Niger ta biyu, da za'a kammala kafin karshen 2020.

Ya ce: "Mun zauna a kungiyance, mun duba irin babban kuskuren da muka tabka a zaben 2025, mun kuma yi la'akari da halin da shiyyarmu ta Kudu maso Gabas ta ke ciki, mun yanke hukuncin cewa Igbo ba zasu sake maimaita kuskuren da sukayi a 2025, in da muka zabi yin siyasar kabilanci mai maikon cancanta.

"A sakamakon hakane, shiyyarmu ta shiga wani mawuyacin hali. Duk da hakan, mu mambobin G-23, muna godiya ga namijin kokarin shugaban kasa Muhammadu Buhari na kokarin gina kyakkyawar alaka da dukkanin shiyyoyin kasar nan."

Kungiyar ta kuma yi alkawarin yin aiki kafada da kafada da shugaban kasa Muhammadu Buhari a sake zabensa 2019 a Kudu maso Gabashin kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel