Dambarwan Siyasa: Rikici ya kunno kai tsakanin Kwankwaso da Shekarau, Wali

Dambarwan Siyasa: Rikici ya kunno kai tsakanin Kwankwaso da Shekarau, Wali

- Komawar Kwankwaso PDP, an fara samun matsala da shi, cewar Shekarau

- An sauke dukkan shugabannin jam'iyyar PDP a jihar Kano

Wata daya bayan sauya shekan Sanatan Rabi’u Musa Kwankwaso zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) daga All Progressives Congress (APC), rikici ya kunno kai cikin sashen jam’iyyar PDP a jihar Kano.

Wannan rikici ya fara ne a lokacin da jam’iyyar PDP ta kasa ta sauke dukkan shugabannin jam’iyyar a jihar da kuma nada sabbin wadanda za su jagoranci mambobin jam’iyyar.

Rikici ya barke ne musamman tsakanin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da wasu manyan jigogin jam’iyyar PDP a jihar wadanda suka kunsho tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau, Ambasada Aminu Wali, Sanata Bello Hayatu Gwarzo da sauran su.

Lokacin da Kwankwaso ya koma jam’iyyar, Shekarau ya bayyana tsoron kada ya zo ya rusa jam’iyyar da suka kasance suna ginawa tun lokacin da ya bar jam’iyyar a 2015.

KU KARANTA: Buhari ya gana da yan Najeriya a kasar Sin

Shekarau ya bayyana hakan ta mai magana da yawunsa inda yace: “Ina sa ran gyararren Kwankwaso ya dawo PDP. Ina sa ran a wannan karon, ba ai bi dokokin jam’iyyar PDP, ba zai maimaita abinda yayi a shekarar 2015 ba lokacin da ya shiga APC.”

Game da labarin da manema labarai suka samu daga majiya mai inganci, rikici ya kunno kai ne makonni uku da suka wuce lokacin da Kwankwaso ya laburta a wani ganawan masu ruwa da tsakin jam’iyyar cewa hedkwatan jam’iyyar PDP ta bashi kujeru 51 na jam’iyyar.

Wannan abu da ya laburta a gaban Shekarau, Wali da Gwarzo da wasu masu fada a ji, bai musu dadi ba kuma sun nuna rashin yardarsu da hakan. Kawai sai Kwankwaso ya fice daga ganawar.

Da manema labarai suka tuntubi Malam Ibrahim Shekarau, mai magana da yawunsa ya ce wannan abin takaici ne saboda Kwankwaso ya fara tada kura a jam’iyyar kamar yadda suke zato.

Yace” Da takaici, Kwankwaso ya fara nunawa jam’a cewa har yanzu bai canza ba.”

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel