Wuta daga sama: Sojin saman Najeriya sun yi wa 'yan Boko Haram mummunar illa
- Sojin saman Najeriya sun yi wa 'yan Boko Haram mummunar illa
- Hakan ta faru ne sakamako wani artabu da sukayi a garin Zari
- An kwace motoci da muggan makaman yan ta'addan
Jami'an rundunar sojin saman Najeriya dake a cikin rundunar hadakar fatattakar 'yan Boko Haram ta 'Lafiya Dole ta sanar da samun gagarumar nasara akan 'yan ta'addan a garin Zari dake a kan iyaka da tafkin Cadi, jihar Borno.

Asali: Depositphotos
KU KARANTA: Zaben 2019: Hafsan sojin Najeriya ya gargadi yan siyasa
Jami'ain hulda da jama'a na rundunar Air Commodore Ibikunle Daramola shine ya sanarwa da manema labarai hakan a ranar Juma'ar da ta gaba a garin Abuja babban birnin tarayya.
Legit.ng ta samu cewa kamar yadda ya shaidawa manema labaran, jami'an sojin saman sun samu nasarar ne a wani artabu da sukayi da 'yan Boko Haram din a ranar Alhamis din da ta gaba.
Air Commodore Ibikunle Daramola ya kuma kara da cewa sun kwace motoci da wasu mugganan makamai da dama daga hannun 'yan ta'addan.
A wani labarin kuma, Gwamnatin tarayyar Najeriya a karkashin jagorancin Shugaba Buhari ta ce ta kammala wani cikakken daftari dake dauke da tsare-tsaren yadda za'a habaka yankin Arewa maso gabas da 'yan ta'addan Boko Haram suka kassara.
Wakilin Najeriya na din-din-din a majalisar dinkin duniya Farfesa Tijjani Bande shine ya sanar da hakan a lokacin da yake tattaunawa da wasu mahalarta taron lalubo hanyoyin tabbatar da zaman lafiya da kuma farfado da tafkin Cadi na majalisar.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng