Katobara: Wani mazaunin jihar Borno ya fitar da hasashen sakamakon zaben 2019, jiha bayan jiha

Katobara: Wani mazaunin jihar Borno ya fitar da hasashen sakamakon zaben 2019, jiha bayan jiha

- Wani mazaunin jihar Borno mai suna Baba Gana Kachalla, ya fitar hasashensa na yadda sakamakon zaben shugaban kasa a 2019 zai kasance

- Hasashen Baba Gana Kachalla ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne zai samu nasara a zaben

- A baya bayan nan, wata hukuma mai hasashen zabuka dake da zama a kasar turai, Zeus Polls, suka fitar da nasu hasashen, inda suka ce Buhari zai lashe zaben 2019

A ci gaba da fuskantar babban zaben 2019 da za'a yi a Nigeria, an samu bulluwar hasashe-hasashe akan yadda sakamakon zaben zai kasance, da kuma makomar jam'iyyu dama yan siyasa a bayan zaben.

A baya bayan nan, wata hukumar hasashen sakamakon zabe mai zaman kanta dake nahiyar turai, Zeus Polls, ta fitar da hasashe kan cewa dan takar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Muhammadu Buhari ne ke da kaso mafi rinjaye na alkaluman zabe a jihohin kasar, a zaben 2019 dake gabatowa.

Hukumar ta Zeus Poll, ta yi hasashen nasarar Willie Obiano na jihar Anambra, da kuma Kayode Fayemi, wanda hasashen nasu ya zamo gaskiya.

KARANTA WANNAN: Da dumi dumi: PDP ta bukaci wasu yan takar shugaban kasa a jam'iyyar da su janye kudurinsu - Majiya

Wannan hasashe na baya bayan nan da Zeus Poll ta fitar, bisa sa hannun Tanko Suleiman, jami'in gudanarwar hukumar a Berlin, kasar Jamus, an raba shi ga manema labarai a Legas, ranar Talata 28 ga watan Augusta.

Ana cikin hana ne kuma sai ga wani mazaunin jihar Borno, da aka bayyana sunansa da Baba Gana Kachalla, ya fitar da nasa hasashen zaben shugaban kasa a 2019, wanda zai gudana jiha bayan jiha, kamar dai yadda ya wallafa wannan hasashe a shafinsa na Facebook.

A cewar hasashen Kachalla, shugaban kasa Muhammadu Buhari ne zai lashe zaben shugaban kasar a 2019.

Wani mazaunin jihar Borno ya fitar da hasashen sakamakon zaben 2019, jiha bayan jiha
Wani mazaunin jihar Borno ya fitar da hasashen sakamakon zaben 2019, jiha bayan jiha
Asali: Facebook

Ga dai yadda hasashen sakamakon zaben zai kasance kamar yadda Kachalla ya wallafa:

Jihar Abia - APC 45%, PDP 55%

Jihar Adamawa - APC 90%, PDP 10%,

Jihar Akwa Ibom - APC 60%, PDP 40%,

Jihar Anambra - APC 70%, PDP 30%

Jihar Ekiti - APC 80%, PDP 20%

Jihar Bauchi - APC 90%, PDP 10%

Jihar Bayelsa - APC 30%, PDP 70%

Jihar Benue - APC 60%, PDP 40%

Jihar Borno - APC 98%, PDP 2%

Jihar Cross River - APC 50%, PDP 50%

Jihar Delta - APC 50%, PDP 50%

Jihar Edo - APC 90%, PDP 10%

Jihar Ebonyi - APC 30%, PDP 70%

Jihar Enugu - APC 30%, PDP 70%

Jihar Gombe - APC 95%, PDP 5%

Jihar Imo - APC 70%, PDP 30%

Jihar Jigawa - APC 90%, PDP 10%

Jihar Kaduna - APC 89%, PDP11%

Jihar Kano - APC 95%, PDP5%

Jihar Katsina - APC 98%, PDP 2%

Jihar Kebbi - APC 95%, PDP5%

Jihar Kogi - APC 80%, PDP 20%

Jihar Kwara - APC 70%, PDP 30%

Jihar Legas - APC 97%, PDP 3%

Jihar Nasarawa - APC 85%, PDP 15%

Jihar Niger - APC 90%, PDP 10

Jihar Ogun - APC 90% PDP 10%

Jihar Ondo - APC 80%, PDP 20%

Jihar Osun - APC 70%, PDP 30%

Jihar Oyo - APC 90%, PDP 10%

Jihar Filato - APC 80% PDP 20%

Jihar Rivers - APC 60% PDP 40%

Jihar Sokoto - APC 90%, PDP 10%

Jihar Taraba - APC 90%, PDP 10%

Jihar Yobe - APC 98%, PDP 2%

Jihar Zamfara - APC 98%, PDP 2%

FCT Abuja - APC 80%, PDP 20%

A baya Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa Chris Ngige, Ministan kwadago, ya ce zaifi dai kabilar Igbo ta zabi Buhari a zaben 2019, saboda alamu na nuna cewa duk ta yadda aka buga, Buhari ne zayyi nasara.

Ya ce al'ummar Igbo nafama da wasu tsauraran ra'ayoyi da ke jefa su cikin mawuyacin hali, wanda sukan kasa fita daga ciki ko da kuwa sun samu damar yin hakan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel