Shugaba Buhari ya isa 'Kasar Sin da safiyar yau ta Asabar
Mun samu cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya isa birnin Beijing na kasar Sin a safiyar yau ta Asabar domin halartar taron hadin kan kasar da kuma nahiyyar Afirka karo na bakwai da za a gudanar a ranakun 3 da 4 ga watan Satumba.
Hadimin shugaban kasar na sabuwar hanyar sadarwa, Bashir Ahmad, wanda ya kasance cikin tawagar shugaban kasar shine ya bayyana wannan sabon rahoto a shafin sa na dandalin sada zumunta.

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, shugaba Buhari yayi bankwana da birnin Abuja a ranar Juma'a da gabata inda ya nufaci Birnin Sin bayan ganawar sa da shugaban kasar Jamus, Angela Merkel a fadarsa ta Villa.
KARANTA KUMA: 'Yan Siyasa 8 da ake zargi da rashawar N232bn kuma suke fafutika akan tazarcen Buhari
Cikin wata sanarwa a ranar 30 ga watan Agustan da ta gabata, kakakin shugaban kasa, Mallam Garba ya bayyana cewa, shugaba Buhari zai gana da shugaban kasar na China, Xi Jin Ping, tare da sauran shugabannin Afirka kafin gudanar da babban taron.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng