Abin da ya sa ba zan shiga kamfanin Nollywood ba – Fati Shu'uma

Abin da ya sa ba zan shiga kamfanin Nollywood ba – Fati Shu'uma

Jarumar fina-finan Hausa, Fati Abubakar, da aka fi sani da Fati Shu'uma ta ce tana kishin fina-finan Hausa don haka ba ta sha'awar fara yin fina-finan harshen Inglishi wato Nollywood wadanda ake yi a kudancin Najeriya.

Jarumar ta shaida wa wakilin BBC Pidgin Mansur Abubakar hakan ne a Kano lokacin da ake daukar wani sabon fim mai suna Makanta Biyu.

Akwai 'yan wasan fina-finan Hausa da ke fitowa a fina-finan Nollywood ciki har da Ali Nuhu da Rahama Sadau da Hadiza Gabon da sauransu.

A fim din dai na Makanta Biyu, Fati ta fito ne a matsayin makauniya wadda ta hadu da wani mai attajiri, Ali Nuhu, wanda sonta ya kama shi.

KU KARANTA: Jami’an yan sanda sun damke budurwa mai kwace baburan yan babur

Daga nan ne ya fara taimaka mata da iyayenta kuma ya taimaka mata da kudin da aka yi mata maganin makantar da ke damunta.

Amma bayan da Fati ta fara gani, sai ta juya wa attajirin baya, wato ta saba wa umarnin iyayenta ke nan.

Sakamakon haka, Ali Nuhu ya koma ya auri kanwarta. Makantar Fati kuma ya dawo.

Hamza Lawal Abubakar wanda shirya fim din ya ce sakon da fim yake isawarsa shi ne illolin rashin biyayya ga iyaye.

Babangida Bangis shi ne wanda ya ba da umarni a fim din ya ce sabon fim din zai shiga kasuwa ne nan da watanni biyu zuwa uku.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel