Dubun wani dan damfara a dandalin sadarwar zamani na Fesbuk ta cika a Najeriya

Dubun wani dan damfara a dandalin sadarwar zamani na Fesbuk ta cika a Najeriya

- Dubun wani dan damfara a dandalin sadarwar zamani na Fesbuk ta cika a Najeriya

- Yan sandan Najeriya suka kama shi a Legas

- Ana tuhumar sa da sace wata yarinya mai shekaru 14

Wani matashi mai shekaru 26 a duniya mai suna Jide Ajayi da ake zargin dan damfara ne ya shiga hannun jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Legas bisa zargin samun sa da laifin guduwa da wata yarinya mai shekaru 14 a duniya.

Dubun wani dan damfara a dandalin sadarwar zamani na Fesbuk ta cika a Najeriya
Dubun wani dan damfara a dandalin sadarwar zamani na Fesbuk ta cika a Najeriya
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: EFCC ta taso wani Sanatan PDP a gaba

Majiyar mu dai ta sanar da mu cewa matashin da kuma yarinyar sun hadu ne a dandanin sadarwar zamani ta Fezbuk kafin daga bisani suyi musayar lambobin waya inda suka rika gaisawa akai-akwai.

Legit.ng ta samu cewa matashin ya je gidan su yarinyar ne mai suna Miracle a cikin satin da ya gabata inda daga nan ne ya tafi da ita zuwa gidan sa da yake zama kuma ya ajiye ta har tsawon kwanaki kafin jami'an 'yan sanda su kamo shi.

Da take maida ba'asi akan yadda lamarin ya auku, yarinyar tace ita dai gaskiya bata san yadda akayi ta tsinci kanta a gidan na sa ba domin tsafi yayi mata ita kuma kawai sai tayi ta bin sa.

'Yan sandan dai sun ce suna kan bincike ne kuma da zarar sun kammala za su kai wanda suke tuhuma kotu domin yanke masa hukunci dai dai da laifin sa.

A wani labarin kuma, Hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Janar Abayomi Olanisakin ya gargadi 'yan siyasar kasa da babbar murya game da neman tada zaune-tsaye a kafin, lokacin da kuma bayan zabukan gama gari da za'a gudanar na shekarar 2019.

Janar Olanisakin ya yi wannan gargadin ne a garin Sokoto inda yaje domin kaddamar da wani sansanin soji na kai agajin gaggawa a barikin sojojin Sama na 119 a kasar dake can garin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel