Katobara: Farfesa Wole Soyinka yayi wa Shugaba Buhari wankin babban bargo

Katobara: Farfesa Wole Soyinka yayi wa Shugaba Buhari wankin babban bargo

- Farfesa Wole Soyinka yayi wa Shugaba Buhari wankin babban bargo

- Soyinka yace sam kalaman na Shugaban basu dace ba

- Shugaba Buhari yace tsaron kasa yafi 'yancin ta

Fitaccen marubucin nan kuma wanda ya taba lashe kambun Laureate, Farfesa Wole Soyinka a ranar Alhamis din da ta gabata ya soki Shugaba Buhari a game da ikirarin da yayi na cewa zaman lafiyar kasa yafi bin dokokin ta muhimmaci a wurin sa.

Katobara: Farfesa Wole Soyinka yayi wa Shugaba Buhari wankin babban bargo
Katobara: Farfesa Wole Soyinka yayi wa Shugaba Buhari wankin babban bargo
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Abu 5 da Saraki yayi alkawari idan ya zama shugaban kasa

Shugaba Buhari din dai ya yi wannan ikirarin ne a cikin jawabin sa na musamman da ya gabatar a wajen babban taron kungiyar lauyoyin Najeriya da suka gabatar a garin Abuja, babban birnin tarayya.

Legit.ng ta samu cewa sai dai da yake mayar da martani game da kalaman na Shugaba Buhari, Farfesa Soyinka ya ce hakan sam bai dace ya fito daga bakin shugaban ba.

Haka zalika ya kuma ce tarihin duniya a ko yaushe ya tabbatar da cewa bin doka da oda ne kadai hanyar tabbatar da zaman lafiya da cigaba a cikin kasa.

A wani labarin kuma, Wani matashi mai shekaru 26 a duniya mai suna Jide Ajayi da ake zargin dan damfara ne ya shiga hannun jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Legas bisa zargin samun sa da laifin guduwa da wata yarinya mai shekaru 14 a duniya.

Majiyar mu dai ta sanar da mu cewa matashin da kuma yarinyar sun hadu ne a dandanin sadarwar zamani ta Fezbuk kafin daga bisani suyi musayar lambobin waya inda suka rika gaisawa akai-akwai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel