An damke wani dan damfara da ke rabon gurraben ayyuka a Jigawa

An damke wani dan damfara da ke rabon gurraben ayyuka a Jigawa

- Hukuma ta damke wani dan damfara da ke sayar da gurabben ayyukan gwamnati a Jigawa

- Matashin, Nasiru Abba, korraren dalibin makarantar koyan aikin jinya ne da ke Jahun a jihar Jigawa

- Asirinsa ya tonu ne bayan mahaifin daya daga cikin wadanda ya yiwa alkawarin bawa aiki ya sanar da hukumar NSCDC

Hukumar tsaro na NSCDC reshen jihar Jigawa bayar da sanarwar damke wani matashi, Nasiru Abba, wanda ya kware wajen damfarar matasa masu neman aiki ta hanyar basu takardun daukan aikin NSCDC amma na bogi.

Kakakin hukumar NSCDC reshen jihar Jigawa, Adamu Shehu, ya ce wanda ake zargin Abba tsohon dalibin makarantar koyan aikin jinya ne da aka kora daga makarantar bayan samunsa da aikata wasu laifuka.

"'Yan uwan wanda ake zargin sun shaidawa NSCDC cewa sun dade suna gargadin Abba ya dena halayensa na damfara saboda wata rana hukuma za ta damke shi kuma ya fuskanci hukunci," kamar yadda Shehu ya fadawa manema labarai.

An kama wani saurayi da ke sayar wa mutane guraben aiki na bogi
An kama wani saurayi da ke sayar wa mutane guraben aiki na bogi
Asali: Twitter

Dubun Abba ta cika ne yayin da mahaifin wani matashi da Abba ya bukaci ya biya shi N120,000, kafin ya kawo masa takardan aikin ya kai kara ofishin NSCDC saboda bai amince da yadda lamarin ke tafiya ba.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun damke wata budurwa da ke yiwa 'yan achaba fashi a Katsina

"Tun da farko, matashin ya karbi N1,700 daga hannun matashin a matsayin kudin fom, daga nan ne akayi masa dabara aka bukaci ya taho da takardun samun aikin domin ya karbi kudin amma da isowarsa sai jami'an NSCDC suka kama shi," inji Adamu Shehu.

"A lokacin da aka kama wanda ake zargin, an same shi da takardun samun aiki na hukumar tsaro ta NSCDC dauke da sunnan wani Yahaya Sambo da Musa Inuwa.

Bayan an fara binciken wasu 'yan uwa biyu, Idris Isa da Isma'ila Isa sun gabatar da takardan aikin bogi da wanda ake zargin ya basu na hukumar kula da shige da fice na kasa Immigration.

Sunce Abba ya umurci su biya shi N120,000 kowannensu kuma tuni har sun biya shi N20,000.

Kakakin hukumar ya yi amfani da wannan damar wajen gargadin matasa su guji fadawa hannun irin wadandan 'yan damfarar da ke karyar samarwa mutane aiki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel