Duniya ba matabbata ba: Alhazawan Najeriya 3 sun mutu akan hanyar Madina zuwa Makkah

Duniya ba matabbata ba: Alhazawan Najeriya 3 sun mutu akan hanyar Madina zuwa Makkah

Ajali aka ce idan yayi kira ko babu ciwo sai an je, a yayin da aka karkare aikin Hajji, mahajjata daga dukkanin fadin Duniya suna komawa gidajensu, wasu kuwa lokacinsu ne ke karewa a kasa mai tsarki, musamman yadda alhazawa ke gamuwa da ajalinsu.

Jaridar premium times ta ruwaito an samu wani mummunan hadari a babbar hanyar data taso daga Madina zuwa birnin Makka, wanda yayi ajalin mutuwar mutane da dama, daga cikinsu har da yan Najeriya mutum uku.

KU KARANTA: Muhimman abinda suka tunzura ni nake neman ɗarewa kujerar shugaban kasa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban tawagar ma’aikatan kiwon lafiya na Najeriya, Ibrahim Kana ne ya tabbatar da mutuwar mahhajatan, inda yace hadarin ya faru ne a ranar Juma’a 31 ga watan Agusta.

“Mun samu labarin wani mummunan hadari daya rutsa da alhazan mu akan hanyar Madina zuwa Makkah, kimain kilomita 120 nesa daga birnin Madina.” Inji Dakta Ibrahim Kana.

Mutanen da suka mutu sun hada da Shinkafi Mudi Mallamawa, wanda aka haifa 10/02/1952, lambar fasfo: A09413309; Abdullahi Jafaru Gidan Sambo, wanda aka haifa a 03/07/1956, lambar fasfo: A09413813; da Abdullahi Shugaba da aka haifa a 22/05/1963, lambar fasfo: A50080535.

A jawabinsa, shugaban kungiyar yan jarida reshen jahar Zamfara, Abdulrazak Kaura yace mamatan shuwagabannin jam’iyyar APC ne a kananan hukumomin Zamfara,

“Jafarau Gidan Sambo shine shugaban APC a karamar hukumar Kaura Namoda, Mudi Mallamawa karamar hukumar Shinkafi, sai Abdullahi Shugaba Ruwan Dorowa na karamar hukumar Maru” Inji shi.

Idan za’a tuna Legit.ng ta ruwaito labarin wani mahajjacin Najeriya daya fuito daga jahar Neja, wanda ya rasu a garin Makkah sakamakon fadawa cikin ramin na’aurar dake kai kawo da mutane a manyan gidajen sama (Lifter).

Wannan mutuwar ta kawo adadin yan Alhazawan Najeriya da suka rasu a yayin aikin Hajji zuwa mutum goma, fatanmu anan shine Allah ya jikansu da gafara, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da Imani.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel