Zaben 2019: Atiku Abubakar ya goga gemu da gemu da IBB, Abdulsalam (Hotuna)
Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar shugaban kasa a jam’yyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya kai ziyarar girmamawa ga tsofaffin shuwagabannin kasar Najeriya dake zaune a garin Minnan jahar Neja.
Jaridar Sahara reporters ta ruwaito a ranar Alhamis, 30 ga watan Agusta ne Atiku ya kai wannan ziyarar ga janar Ibrahim Badamasi Babangida a gidansa dake kan tsauni a Minna, inda suka sanya labule ba tare da an ji abinda suka tattauna ba.
KU KARANTA: Jami’an kwana kwana sun ceto wani mutumi yayin da gidan sama ya ruguzo a Kano

Asali: Depositphotos
Hakalika majiyar Legit.ng ta ruwaito jim kadan bayan Atiku ya gana da IBB, sai ya wanke kafafunsa ya garzaya gidan tsohon shugaban kasa na mulkin Soja Abdulsalami Abubakar, inda anan ma suka goga gemu da gemu.
Ziyarar da Atiku ya kai jahar Neja ya kai ta ne da nufin ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a jahar, wanda ya bayyana tattaunawar tasa da irin kyakkyawar tarbar daya samu a matsayin wani muhimmin abu a gareshi.

Asali: Twitter
Idan za’a tuna a ranar 1 ga watan Yuli tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kai ma IBB ziyara, wanda hakan ya kawo adadin ziyarar da Atiku ya kai ma IBB a shekarar nan zuwa biyu.
Masana al’amuran siyasa na ganin manuniya ta nuna tsohon shugaban kasa IBB na mara ma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku baya a kokarinsa na zama shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng