Yadda Rarara yayi sama da Naira Miliyan 200 da aka rabawa Mawakan APC

Yadda Rarara yayi sama da Naira Miliyan 200 da aka rabawa Mawakan APC

Labari ya zo mana daga Jaridar Concord Times cewa Mawakin nan Adamu Dauda Kahutu wanda aka fi sani da Rarara yayi gaba da wasu kudi da manyan motoci aka ba Mawakan da ke Arewacin Najeriya.

Yadda Rarara yayi sama da Naira Miliyan 200 da aka rabawa Mawakan APC
Dauda Rarara da wasu Mawaka tare da Gwamnan Kaduna Hoto: Concord Times
Asali: UGC

Kamar yadda mu ka samu labari, Dauda Adamu Rarara yayi gaba da wasu Naira Miliyan 200 ne da aka ba Mawakan da su ka yi wa Shugaban kasa Buhari waka a 2015. Shi dai Rarara yayi sama da fadi da wadannan miliyoyi da su ka shigo hannun sa.

Daya daga cikin Mawakan da aka shirya ba wannan kudi mai suna Ibrahim Yala ya bayyanawa Concord Times cewa Rarara ya sha kwana da kudin na su. Yala yana cikin masu yi wa Shugaba Buhari da kuma wani na hannun daman Nasir El-Rufai waka.

Mawakin yace manyan Gwamnonin APC irin su Aminu Masari da Nasir El-Rufai da kuma Abdulazi Yari ne su ka ba su motoci da kudi har sama da Naira miliyan 45 a 2015 domin ayi wa Buhari waka. An dai ajiye wannan kudi ne a cikin asusun Rarara.

KU KARANTA: Abubuwa 6 da Kwankwaso ya fada wajen kaddamar da shirin takarar 2019

Bayan nan kuma Mawakan sun samu gudumuwar kudi har kusan Naira Miliyan 180 da kuma manyan motoci da dama. Sai dai yanzu Rarara yayi gaba da wadannan kudi da ke cikin asusun sa inda ya bar sauran Mawakan ‘Yanuwan sa da hamma inji Yala.

Ibrahim Yala ya fadawa Jaridar Concord Time cewa yanzu Rarara yayi gaba da wadannan miliyoyi yayin da ya maida motocin na sa da kuma yaran sa. Yala yace Rarara dai ya rantse cewa ba zai bada wannan kudi ba komai zai faru domin tuni ma dai ya kashe su.

Wani Mawakin dai ya bayyana cewa Rarara ya munafunce su bayan yayi gaba da abin da su ka samu a lokacin yakin neman zaben 2015. Har yanzu dai Rarara wanda tauraruwar sa ta ke haskawa bai ce komai game da wannan zargi ba kuma ba ya daukar waya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng