Shugaba Buhari ya bar Najeriya zuwa China
A gobe Juma'a 31 ga watan Augusta ne aka sa ran shugaba Muhammadu Buhari zai tafi kasar China domin hallarton taron hadin kai tsakanin nahiyar Afirka da China a turence 'Forum on China-African Cooperation' (FOCAC) wanda za'ayi daga ranar 3 zuwa 4 ga watan Satumba a birnin Beijing.
Wannan sanarwan ta fito ne daga bakin mai taimakawa shugaban kasar ta fanin kafafen yadda labarai, Femi Adesina ta shafinsa na Facebook.
Da isar sa kasar, shugaba Muhammadu Buhari zai gana da al'ummar Najeriya mazauna kasar China a ofishin jakadancin Najeriya da ke China.

Asali: Depositphotos
DUBA WANNAN: A karo na farko bayan tsige shi, Lawal Daura ya yi magana kan mamaye majalisa
Kafin fara taron na FOCAC, a matsayin na shugaban kungiyar kasashen Afirka (ECOWAS)shugaba Buhari zai yi jawabi a wani taron shugabani nahiyar Afirka da China tare da masu 'yan kasuwa da masu masana'antu a Afirka.
Daga baya, shugaba Buhari zai hadu tare da takwaransa na China, Shugaba Jinping tare da sauran shugabanin kasashen Afirka inda zau tattauna a kan maudu'in taron na FOCAC na shekarar 2018 mai taken 'Toward an even Stronger China-African Community with a shared Future."
Shugaba Buhari kuma zaiyi amfani da wannan damar don ganawa da shuganin China inda zasu bayyana masa irin nasarorin da aka samu wajen ayyukan cigaba kamar gine-gine, aikin layin dogo da aikin wutan lantarki da China ke yi a Najeriya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng