Sarkin Kano ya nemi a rika damawa da Almajirai a cikin harkokin boko a Nigeria

Sarkin Kano ya nemi a rika damawa da Almajirai a cikin harkokin boko a Nigeria

- Sarki Sunusi na jihar Kano, ya bayyana muhimmancin samarwa Ilimin Arabi gurbi a tsarin ilimin boko a Nigeria

- Sarkin wanda ya nuna takaicinsa kan yadda aka maida ilimin Arabi saniyar ware ya ce akwai bukatar bunkasa yarukan cikin gida

- Daga karshe Sanusi ya bayyana cewa ana kan yin kokarin mayar da ilimin likitanci, noma, injiniyanci da sauransu zuwa harshen Hausa.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya bayyana bukatar sake fasalin ilimin boko a kasar don cusa na addinin Arabi a ciki dama sanya ilimin harsunan gargajiya a manyan makarantu, yana mai cewa dogaro da turanci zai taimakane kawai wajen kawo rashin ci gaba a kasar.

Sanusi ya kuma yi jawabi na kalubalantar irin tsattsauran matakin da tsarin ilimin boko a kasar ya dauka na nuna ko ‘Oho’ da karatun Arabi, idan aka zo fagen daukar aiki da bada guraben karatu a manyan makarantu.

Ya yi wannan kiran ne a Kano, wajen taron kaddamar da wani littafi tare da ‘Film’ cikin harshen Hausa, wanda wata yar kasar Belgium, Hannah Hochner ta rubuta, akan halin da Almajirai ke tsintar kawunansu a kokarin neman ilimin Arabi a jihohin Arewa.

Ya bayyana damuwa da rashin jin dadinsa akan yadda akayi watsi da matsayin karatun Arabi dana Al-Qur’ani, duk da cewa ilimin ya riga na boko zuwa kasar.

Sarkin Kano ya nemi a rika damawa da Almajirai a cikin harkokin boko a Nigeria
Sarkin Kano ya nemi a rika damawa da Almajirai a cikin harkokin boko a Nigeria
Asali: Facebook

KARANTA WANNAN: Sabon bincike: Awaki na iya banbance mutane masu fushi da masu fara'a

Sarkin ya ce kasashe da dama sun samu ci gaba, saboda suna amfani da yarukansu wajen koyarwa a makarantu, inda suke amfani da yaren Turanci a matsayin yaren amfani a cikin lamuran yau da kullum

“A yau a Nigeria, kowa na maka kallon jahili ma damar baka iya magana da harshen turanci ba. Wannan ne ya sa a yau, ko wane mataki kakai a fagen ilimin Arabi, zaka ci gaba da kasancewa maras amfani, ma damar zaka biye ta tsarin ilimin zamani na kasar” a cewar Sanusi.

Sarkin sai ya bayyana wani yunkuri da ake kanyi a jami’ar Bayero dake Kano tare da hadin guiwar makarantar koyar da darussa daga Afrika dake birnin Landan, na mayar da wasu muhimman ilimi da suka hada da ilimin na sarrafa magunguna, unguwar zoma, noma da kuma Injiniyanci daga turanci zuwa harshen Hausa don bunkasa yare a idon duniya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel