Garabasa: Hadiman Marafa a APC sun samu kyautar motoci 41

Garabasa: Hadiman Marafa a APC sun samu kyautar motoci 41

- Sanata Kabiru Marafa ya rabawa hadimansa na APC motoci 41

- Haka zalika Sanatan ya rabawa mabukata buhuna 2,000 na hatsi da kyautar Naira dubu daya akan kowane buhu

- Tuni dai Marafa ya bayyana kudirinsana tsayawa takarar gwamnan jihar a zaben 2019 dake gabatowa

Kungiyar yakin neman zaben Sanata Marafa ta rabawa wasu hadimansa dake APC kyautar motoci 41, tare da kuma raba akalla buhunan hatsi 2,000 ga mabukata a jihar Zamfara.

Haka zalika Sanata Kabiru Garba Marafa da ke wakilatar Zamfara ta tsakiya a majalisar dattijai, karkashin jam’iayar APC, ya raba rigunan kwallo guda 100,000 ga magoya bayansa dake a fadin jihar.

Marafa, wanda yake daya daga cikin manyan sanatoci a kasar, shi ne wanda akafi kyautata zaton tsayawa takarar gwamnan jihar ta Zamfara karkashin jam’iya mai mulki ta APC.

Tuni dai ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar gwamnan jihar a zaben 2019 da ke gabatowa, da alkawarin magance matsalar tsaro, bunkasa fannin noma (babbar sana’ar al’umar jihar), da kuma dakile yaduwar talauci a jihar.

KARANTA WANNAN: Sabon bincike: Awaki na iya banbance mutane masu fushi da masu fara'a

A cikin wata sanarwa, Sakataren hulda da jama’a na APC a jihar Zamfara, Bello Soja Bakyasuwa, ya ce tuni aka raa kayayyakin kamar yadda yake a umarce.

Motoci, a cewarsa sun hada da Peugeot 406 guda 24, VW Golf guda 12, Peugeot 407 guda 3, VW Sharon guda 6, Murano guda daya, Highlander guda daya da kuma Bas bas guda 4.

Marafara ya rabawa mabukata buhuna 2,000 na hatsi
Marafara ya rabawa mabukata buhuna 2,000 na hatsi
Asali: Twitter

Ya lissafa wadanda suka ci gajiyar motocin da suka hada da shugaban jam’iyar APC na jihar, mataimakan shugaban jam’iyar na shiyyoyi uku, sakataren jiah, da shugaban matasa.

Sauran sun hada da sakataren gudanarwa, sakataren watsa labarai, shugabar mata, dukkanin shuwagabannin kananan hukumomi da kuma wasu manyan magoya bayansa a jihar.

Ya ce buhunan hatsi 2,000 kuwa, an raba su ne ga mazauna sansanonin gudun hijira, marasa galihu da kuma kungiyoyin matasa na jihar.

Domin saukaka zirga zirgar, kowane buhu na hade da Naira dubu daya, da zasu ishi wadanda suka ci gajiyar tallafin kai kayan gida.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel