Rijistan katin zabe: An bukaci gwamnatin Kwara da ta kaddamar da gobe Juma’a a matsayin ranar hutu

Rijistan katin zabe: An bukaci gwamnatin Kwara da ta kaddamar da gobe Juma’a a matsayin ranar hutu

Shugaban gidauniyar Adekunle Oyedepo Foundation, Mista Adekunle Oyedepo ya bukaci gwamnatin jihar Kwara da ta kaddamar da ranar Juma’a, 31 ga watan Agusta a matsayin ranar hutu domin ba ma’aikatan gwamnati a jihar damar yin rijistar katin zabe da ake ci gaba da yi.

Oyedepo wanda ke neman takarar kujerar dan majalisar jiha na yankin Irepodu a wata sanarwa day a saki a ranar Alhamis yace wannan zai ba ma’aikata da basu yi rijitstan katin zaben su ba damar yin haka kafin ranar karshe da hukumar zabe mai zaman kanta ta bayar na yin hakan.

Ya kara da cewa idan har gwamnati ta bayar da wannan hutu, ma’aikatan da suka yi rijista amma basu samu damar zuwa karban katinsu ba sai suje su karba.

Rijistan katin zabe: An bukaci gwamnatin Kwara da ta kaddamar da gobe Juma’a a matsayin ranar hutu
Rijistan katin zabe: An bukaci gwamnatin Kwara da ta kaddamar da gobe Juma’a a matsayin ranar hutu
Asali: Facebook

Dan takaran ya kuma yi kira ga mutanen Kwara da mazauna jihar da basu riga sun yi rijista ba da suje cibiyar INEC mafi kusa suyi hakan a yan sa’o’in da suka rage domin su mallaki katinsu na zabe.

A cewarsa hakan zai basu damar zabar dan takarar da ransu ke so a zabe mai zuwa.

A wani lamari na daban, Ibrahim Hassan Dankwambo, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Democratic Party (PDP) kuma gwamnan jihar Gombe, ya bayyana cewa baya siyasar ko a mutu ko ayi rai don kawai ya zama dan takara a jam’iyyar a zaben 2019.

KU KARANTA KUMA: Wasu manyan limaman Coci sun shiga hannu bayan sun kashe wata mata

Dankwambo, yayinda yake neman goyon bayan mambobin jam’iyyar da diligit akan kudirinsa na son zama dan takarar jam’iyyar a zabe mai zuwa a ranar Laraba, 29 ga watan Agusta, a Benin, jihar Edo yace zai goyama duk wadda ya zamo dan takara baya idan har aka yi adalci da gaskiya wajen zaben.

Wata kungiya ta bukaci Gwamna Dankwambo da ya yi takarar kujerar shugabancin kasa a 2019. Kungiyar ta Dankwambo Grassroots Networks (DGN) ta bayyana gwamnan a matsayin dan takara daya da ya dace da takara a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel