Rabuwar kai a jam’iyyar APC kan tsarin gudanar da zaben fidda gwani yayinda kwamitin zantarwa za ta gana yau

Rabuwar kai a jam’iyyar APC kan tsarin gudanar da zaben fidda gwani yayinda kwamitin zantarwa za ta gana yau

An samu gagarumin rabuwar kai a jam’iyya mai mulki ta All Progressives Party (APC) kan sabuwar tsarin gudanar da zaben fidda gwani da jam’iyyar ke shirin amfani da shi gabanin zaben 2019.

Majiya a jamiyyar sun bayyanawa jaridar Daily Trust cewa a jiya, yawancin yan jam’iyyar musamman gwamnoni sun nuna rashin yardarsu da bari mambobin jam’iyya gaba daya su kada kuri’a wajen zaben fidda gwani.

Wannan tsari ya fi kwantawa babban jigon jam’iyyar, Bola Tinubu, da shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomole.

Rabuwar kai a jam’iyyar APC kan tsarin gudanar da zaben fidda gwani yayinda kwamitin zantarwa za ta gana yau
Rabuwar kai a jam’iyyar APC kan tsarin gudanar da zaben fidda gwani yayinda kwamitin zantarwa za ta gana yau
Asali: Depositphotos

A yau zata kare inda kwamitin zantarwan jam’iyyar zata gana don kawo karshen muhawaran da kuma shirya yadda za’a gudanar da zaben fidda gwani.

Tinubu da Oshiomole sun yi kokarin gamsar da shugaba Muhammadu Buhari kan muhimmanci barin kowani mamba jam’iyya mai kati yayi zabe amma da alamun gwamnonin na ganin hakan cutane garesu.

KU KARANTA: Na ji dadin zuwana Najeriya – Theresa May

Daya daga cikin gwamnonin ya bayyanawa Daily Trust cewa gwamnonin sun fi son Deleget suyi zaben saboda yanayin rashin tsaro da wasu sassan kasan da kuma tattalin kudi.

Gwamnan yace: “Maganan cewa kwamitin gudanarwan jam’iyyar ta amince da budaddiyar zaben fidda gwani karya ne. kundin tsarin mulkin jam’iyyar ta bada daman budaddiyar zabe da kullaliya. Abinda kwamitin tayi shine baiwa jihohi daman kawo ra’ayinsu kafin a yanke shawara.”

Dukkan gwamnonin Arewa 14 sun bayyana rashin amincewarsu da sabon tsarin. Dalilinsu biyu ne na farko tsadar haka, saboda zai iya kai zaben kasa tsada. Na biyu kuma tsaro.”

Banbanci tsakanin tsarin zabukan guda biyu shine budaddiyar zaben fidda gwani zai rage cin hanci da ake bawa Deleget sannan kowa zai samu yancin zaben wanda zai wakilci jam’iyyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel