Hukumar INEC tasha alwashin gurfanar da duk wanda ta samu da laifin siyen kuri'u

Hukumar INEC tasha alwashin gurfanar da duk wanda ta samu da laifin siyen kuri'u

- Hukumar INEC ta sha alwashin daukar mataki akan duk wanda aka kama da laifin siyen kuri'u

- Hukumar ta ce tuni ta kaddamar da shirin wayarwa jama'a kai dangane da illolin da ke tattare da sayar da kuri'a

- An samu karuwar siyen kuri'u a zaben gwamnonin jihohin Ekiti da Ondo, a cewar wani rahoto

Hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi gargadin cewa zata gurfanar da duk wanda aka kama da laifin yaudarar masu kad'a kuri'a don siyen katin zabensu a zaben gwamanan jihar Osun da za'a gudanar 22 ga watan Satumba.

Mataimakin darakta, a sashen wayar da kan jama'a kan gudanar da zabe na hukumar, Stephen Ojewande, ya bayyana hakan a wata zantawarsa da jaridar The Nation.

Ojewande ya ce dokar zabe ta haramta yaudarar masu kad'a kuri'a ta kowace fuska, kamar yadda sashe na 12 na dokar ya nuna cin tarar N5000,000 ko watanni 12 a gidan yari ga duk wanda aka kama da aikata wannan laifi.

Ya ce karuwar aikata laifin a zabukan baya ne ya sanya hukumar cikin damuwa da kuma daukar tsattsauran mataki don dakile faruwar hakan a nan gaba.

KARANTA WANNAN: PDP ta tsaida dan takarar gwamna da mataimakinsa a jihar Osun

Hukumar INEC tasha alwashin gurfanar da duk wanda ta samu da laifin siyen kuri'u
Hukumar INEC tasha alwashin gurfanar da duk wanda ta samu da laifin siyen kuri'u
Asali: Depositphotos

Mataimakin daraktan ya bayyana cewa tuni an fara gudanar da shirin wayar da kan jama'a dangane da illolin siyen kuri'u, kamar yadda jami'an hukumar ke tunasar da jama'a cewa ba zasu samu gwamnati mai adalci ba idan har ana siyen kuri'un su.

Ya kara da cewa jami'an hukumar na bincike don zakulo duk wani jami'inta da ke da hannu a siyen kuri'u, inda ya kara da cewa za'ayi amfani da dokar data dace. Ya ce hukumar zata ci gaba da wayarwa jama'a kai akan gujewa sayar da kuri'unsu.

Ojewande ya ce: "Karya dokoki hanya ce ta durkushewar ci gaban kasa. Zamu tabbatar da cewa mun kama duk wanda ya sayi kuri'ar wani, saboda aikata hakan ya sabawa doka. Zamu tabbatar mun gurfanar dasu don yanke masu hukunci."

Rahotanni dai sun nuna cewa an samu yawaitar siyen kuri'u a zaben gwamnonin jihohin Ondo da Ekiti da ya gudana.

Dangane da shirye shiryen da INEC ta ke yi, musamman na amfani da na'urar tantance masu zabe, Ojewande yace ana kan gwada dukkanin na'urorin lokaci zuwa lokaci, kana akwai wasu da aka ajiye don gudun bacin rana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel